10 Agusta 2024 - 09:41
An Aika Sakon Barazana Ga Dubunnan Sahyoniyawan: Za A Binne Ku Mako Mai Zuwa

Majiyoyin labarai sun bayar da rahoton aike da sakonnin barazana ga wayoyin salula na dubban yahudawan sahyoniyawan da ke yankunan da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya habarta maku cewa: an aike da sakonnin barazana ga wayoyin hannu ga dubban yahudawan sahyoniyawan da ke zaune a yankunan da aka mamaye, wadanda su ke dauke da sunayensu a cikin wannan sakon.

Acikin Sakon ya zo cewa: Za a binne ku a mako mai zuwa.

'Yan sanda, ma'aikatar sadarwa da watsa labarai da cibiyar yanar gizo ta gwamnatin Sahayoniya sun bukaci yahudawan sahyoniya da su rufe asusun wanda ya aiko da sakon nin zuwa garesu idan zai yiwu.

Hukumomin tsaron yahudawan sahyoniya sun fara gudanar da bincike mai zurfi dangane da hakan.

A baya-bayan nan kuma, cibiyar sadarwa ta "Hadath" ta bayar da rahoton cewa, ta nakalto daga majiyar gwamnatin sahyoniyawan a ranar alhamis cewa ta fice daga hedkwatarta na tsaro da leken asiri har guda hudu da ke birnin Tel Aviv saboda fargabar harin ramuwar gayya daga Iran da Hizbullah.

Damuwa da rashin nutsuwa da zaman dardar tare da rugujewar tunani a gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na karuwa a kowace rana sakamakon irin martanin da Iran za ta aiwatar dangane da kisan gillar da aka yi wa shahid "Isma'il Haniyyah" shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, da kuma martanin gwagwarmayar Musulunci ta Lebanon ga kisan gillar da aka yi wa shahid "Fu’ad Shukri" babban kwamandanta.

Gidan radiyon yahudawan sahyoniya ya tabbatar da cewa bayan kisan shahid Haniyyah, yahudawan sahyoniyawan suna jiran martani kan wannan harin na kisan gilla.

A cewar wannan rahoto, hukumomin leken asiri na gwamnatin sahyoniyawan suna kuma kokarin samun yanayin nau'I da waje da lokacin harin zai kasance da taimakon kawayensu.

A yayin da take ishara da kauracewa tituna da damuwa a fuskokin kowane dan sahayoniya, gidan rediyon yahudawan sahyoniya ya bayyana shi da cewa ya yi kama da yanayin zamanin Corona.