20 Agusta 2024 - 07:19
Hizbullah Ta Kai Harin Makami Mai Linzami  Kan Falasdinu Da Aka Mamaye

Gwamnatin Sahayoniya ta sanar da kai wani kazamin hari da makamin roka da kungiyar Hizbullah ta kai kan yankunan arewacin Palastinu da ta mamaye da suka hada da Gabar Galili da Tuddan Golan.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku bias nakaltowa daga shafin sadarwa na Quds cewa: Tashar talabijin ta 12 ta gwamnatin Sahayoniya ta jaddada cewa an harba rokoki da dama daga kudancin kasar Labanon zuwa arewacin Palastinu da aka mamaye.

Biyo bayan hakan kuma an kunna kararrawar tunatarwa a manyan sassan arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye. Bayan wanna hari gobara ta kama a yankin kuma an bukaci Sahayoniyawan da su tsaya kusa da mafakarsu

Tun a safiyar yau ne kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai wa yankin Falasdinu da yahudawa suka mamaye hari da makami mai linzami har sau 3.

Majiyoyin harshen yahudanci sun ba da rahoton faruwar gobara da dama, ciki har da a yankunan Jadot da Ortal a cikin Golan da aka mamaye.

Karamar hukumar Kiryat Shmona ta kuma bukaci yahudawan sahyoniya da su tsaya kusa da matsugunan mafakarsu kuma kada su yi tafiya a halin yanzu, kamar yadda tantancewar tsaro ta nuna.