21 Agusta 2024 - 07:40
Hizbullah Takai Harin Makami Mai Linzami Da Jiragen Sama Maras Matuki Kan Arewacin Falasdinu Da Aka Mamaye Da Yankin Golan Na Kasar Syria + Bidiyo.

Jaridar yahudawan sahyoniya ta Yediot Aharnot ta bayyana hare-haren na yau da kungiyar Hizbullah ta kai a kasar Labanon a matsayin mai hadari da ba a taba ganin irinsa ba.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku bisa nakaltowa daga kafofin yada labarai da dadama  inda daga cikinsu Aljazeera, ta nakalto daga masu bada taimakon agaji na Isra'ila cewa a yayin harin rokoki da aka kai daga bangaren Lebanon zuwa yankin Golan, ya zuwa yanzu mutum guda ya jikkata.

Rediyon Sojojin Isra'ila: An harba rokoki da dama daga kudancin Lebanon zuwa yankin Golan da aka mamaye. sanna anji  ƙararrawa a cikin Saman Galili (arewacin yankunan da aka mamaye)

Kafofin yada labaran yahudawan sahyoniya sun tabbatar da harba wasu rokoki daga kasar Labanon kai tsaye a gine gine 5 a Golan. Kamar yadda bayan wanna harin Rediyon hukumar Isra'ila ya bada rahoton cewa an rufe tituna da manyan tituna a Golan da aka mamaye. Sannan Hukumomi sun bukaci mazauna yankin Katsrin (a cikin Golan da aka mamaye) da su fake a wuraren da aka karewa.

Kafofin yada labaran cikin gidan yahudawan sahyoniya suna mai da martani kan harin da kungiyar Hizbullah ta kai a safiyar yau a kasar Labanon: Mista Ministan Tsaro [Yaki] Barka da safiya!

Da yake la'akari da gazawar sojojin gwamnatin mamaya wajen tinkarar makamai masu linzami na Hizbullah, kafofin yada labarai na cikin gida da ke da alaka da 'yan sahayoniyawan sun yi wa ministan yakin gwamnatin sahyoniya ba'a tare da yi masa jawabi kamar haka: "Mai ministan tsaro [yaki], barka da safiya!"

Ita ma jaridar yahudawan sahyoniya ta Yediot Aharnot ta bayyana hare-haren na yau da kungiyar Hizbullah ta kai a kasar Labanon a matsayin mai hadari da ba a taba ganin irinsa ba.