10 Agusta 2024 - 19:52
Mummunan Harin Kare Dangin Da Yahudawan Sahyoniya Suka Aikata A Gaza A Yau; Sama Da Mutane 100 Ne Suka Yi Shahada + Hotuna

Dakarun gwamnatin sahyoniyawan sun sake yin wani aika-aikar ta’addanci a Gaza a safiyar yau Asabar, inda mutane da dama kusan 150 suka yi shahada tare da jikkatar wasu.

Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA- ya bayar da rahoton cewa: sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a makarantar Tabi'in da ke yankin Al-Darj da ke tsakiyar birnin Gaza a lokacin sallar asuba

A cewar ma’aikatar agaji ta Gaza, kimanin Palasdinawa 100 ne suka yi shahada tare da jikkata wasu da dama a wannan danyen aikin, sakamakon gobarar da ta tashi a wannan makaranta sakamakon tashin bam din, gawarwakin shahidai da dama ne suka kone, ina da jami’an agaji su kai kokarin shawo kan gobarar domin ceto wadanda suka jikkata tare da fitar da gawarwakin shahidan daga karkashin baraguzan ginin.

Wannan Ma’aikar ta sanar da cewa gawarwakin da dama daga cikin wadanda suka yi shahada a harin bam din da aka kai a makarantar Tabi'in da ke birnin Gaza sun rugurguje sun daidaice kuma ba a gane su wajen tantancewa. Galibin wadanda wannan harin ta’addancin ya shafa yara ne da kuma tsofaffi.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa laifin kai harin bam a makarantar Tabi'een da ke unguwar al-Darj a cikin birnin Gaza ci gaba ne da kisan kiyashin da yahudawan sahyoniyawa suka yi wa al'ummar Palastinu kuma gwamnatin Amurka na da hannu wajen aikata wadannan laifuka.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, wannan yunkuri ya jaddada cewa harin bam da aka kai a makarantar Tabi’een babban laifi ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tabarbarewar laifuka da kashe-kashen da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin yake-yake, wadanda yahudawai suke aiwatarwa a zirin Gaza.

A cikin wannan bayanin an bayyana cewa, wannan danyen aiki da kisan kiyashi da aka yi wa fararen hula Falasdinawa a wata makaranta mai cike da 'yan gudun hijirar Palasdinawa da sojojin yahudawan sahyoniyawan suka yi a lokacin sallar asuba, inda sama da mutane 100 suka yi shahada tare da jikkata wasu da dama, ta yadda da dama daga cikin su  ba za’a iya gane jikinsu ba, a fili yake ba da muhimmanci ga ci gaba da aiwatar da kisan gillar da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa al'ummar Palastinu a zirin Gaza ta hanyar ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula Palasdinawa a cibiyoyin tsugunar da 'yan gudun hijira da yankunan da suke zaune tare da aikata munanan laifuka a kansu.

Nasir Kan’ani kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya dauki wannan harin na dabbanci a matsayin misali karara na aikata laifukan kisan kare dangi da laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a lokaci guda.

Ya kuma jaddada cewa: Ci gaba da hare-haren hauka da gwamnatin sahyoniyawa suke yi kan al'ummar Palastinu da kuma kisan gilla da ake yi wa mata da yara da tsofaffi, musamman ma a yau munanan harin da wannan gwamnati ta kai kan 'yan gudun hijirar Palastinawa da ke zaune a makarantar Tabi’in, ya sake tabbatar da cewa; mulkin wariyar launin fata na Isra'ila ba ya bin kowace doka da ka'idojin dokokin kasa da kasa.