24 Agusta 2024 - 06:51
Hizbullah Ta Kai Harin makami mai linzami kan sansanin "Maroon".

Majiyar Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, kungiyar Hizbullah ta kai hari kan wani sansanin sojin sama na gwamnatin sahyoniyawan da manyan makamai masu linzami a arewacin Palastinu da ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku cewa: Kafofin yada labaran Isra'ila sun buga wasu hotuna a safiyar jiya (Juma'a) da suka nuna cewa sansanin sojin saman IBA da ke tsaunin Meron a arewacin Falasdinu da ta mamaye yana cin wuta.

Bayan 'yan mintoci kaɗan, majiyoyin labarai sun ba da rahoton cewa, wasu makamai masu linzami sun afka wa wannan sansanin. Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa wadannan makaman sun yi barna sosai ga wannan sansanin bayan wannan harin.

Wani jami'in tsaron Isra'ila ya tabbatar da hakan a wata hira da gidan rediyon sojojin Isra'ila "Golgeltz" cewa, Hezbollah ta kai hari kan sansanin sojin saman "Maron" da makamai masu linzami dama kuma makaman sun afkawa wannan sansanin.

Rundunar sojin Isra'ila ba ta fitar da wata sanarwa ba game da adadin barnar da aka yi wa wannan sansani da kuma asarar rayuka har zuwa lokacin da aka buga wannan rahoto.

A ci gaba da goyon bayan al'ummar Palasdinu, kungiyar Hizbullah ta kai hare-hare kan wuraren da sojojin gwamnatin sahyoniyawan da ke arewacin Palastinu ta mamaye fiye da sau 2,500 a cikin watanni 10 da suka gabata.

Dakarun Lebanon sun sanar da cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan har sai gwamnatin sahyoniyawan ta daina kai hari a zirin Gaza.