25 Agusta 2024 - 10:24
Hizbullah: Mun Yaudare Sojojin Isra'ila Da Makami mai linzami/Mun Kai Hari Muhimman Wurare 2 A Tel Aviv

Hizbullah tace sun yaudari sojojin Isra'ila da makamai masu linzami inda suka kai hari a muhimman wurare guda biyu a Tel Aviv

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti As Abna ya habarto maku bisa nakaltowa daga shafin IRNA cewa: Majiyar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da cewa, a matakin farko na martanin kan kisan gillar da aka yi wa babban kwamandan kungiyar Jihadi Fu'ad Shukri ta kai hari kan muhimman wurare a arewacin birnin Tel Aviv.

Kamfanin dillancin labarai na IRNA na kasar Iran ya habarta cewa, majiyar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta shaidawa tashar Al-Arabi cewa: Isra'ila ta gaza kare harin bazatar da mu ka yi kuma wannan hari da Isra'ila ke magana a kai na mayar da martani ne ga wani harin da mu ne muka kai shi.

Majiyar ta ci gaba da cewa: Sojojin Isra'ila sun gaza gano da kakkabo jiragen mu marasa matuka, kuma mun yi nasarar yaudare sojojin Isra'ila ta hanyar harba makamai masu linzami.

Ya kuma sanar da cewa: Mun kai hari kan manyan wurare guda biyu a arewacin Tel Aviv, wadanda za mu sanar nan gaba.

Wannan majiyar ta ci gaba da cewa: A harin da Isra'ila ta kai kan wurare sama da 30, ba mu da shahidai saboda mun kwashe su kowa daga wajen. Sojojin gwamnatin mamaya sun mayar da martani kan harin da mu kai da hare-haren nasu, kuma a dalilin haka ne jiragen mu marasa matuka suka yi iya bi tare da wuce ta sararin samaniyar yankin.

Ya kuma jaddada cewa: An yi watsi da ikirarin da sojojin Isra'ila suka yi na kawar da wannan hari sakamakon nasarar shigar da jiragen mu marasa matuka masu dauke da makamai suka kai.

Dangane da haka ne kuma kafar yaɗa labarai ta Al-Mayadeen ta ruwaito cewa: Gwagwarmayar Musulunci ta kai hari kan wata muhimmiyar cibiya ta soji a cikin yankunan da aka mamaye ta kai hari kwara takwas kuma a wajenta.

Al-Mayadeen ta sanar da cewa: Martanin gwagwarmaya kan kisan shahida Fu'ad Shukri ya yi nasara duk da cikakken gargadin da Isra'ila ta yi sama da wata guda. Jigon harin gwagwarmaya dai shi ne jirage marasa matuki da suka kai hari kan wani muhimmin sansanin soji sannan sun harba makamai masu linzami 320 don karkatar da tsarin Iron Dome da sauran kayayyakin kare hari.

A safiyar yau ne kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da kammala matakin farko na mayar da martani kan kisan kwamandanta na jihadi Fu'ad Shukri.

A wannan mataki na mayar da martani, Hizbullah ta kai hari kan sansanoni 11 da wuraren soji na gwamnatin sahyoniyawan.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara da cewa, tun bayan fara ayyukan kungiyar Hizbullah a yankin arewacin kasar Palastinu da a mamaye, an tilastawa dimbin sahyoniyawa mazauna wannan yanki barin gidajensu, kuma kamar yadda kafafen yada labaran yahudawan sahyuniya suka ruwaito, galibin sauran mazauna wannan yanki ne suna fama da matsalolin rayuka da tunani.

A halin da ake ciki dai damuwar yahudawan sahyoniyawa da rudanin tunani game da hakikanin martanin da Iran zata ta mayar dangane da kisan gillar da aka yi wa shahid "Isma'il Haniyyah" shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas da kuma martanin da juriyar Musulunci ta Lebanon ta yi kan kisan gillar da aka yi wa da gwagwarmaya Shahid “Fu'ad Shukri” babban kwamandanta ya kara wa wadannan matsalolin kwakwalwa yawa.

Kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya sun tabbatar da cewa bayan kisan Shahida Haniyyah da Fu'ad Shukri, yahudawan sahyuniya na jiran martani kan wannan farmaki na kisan gilla.