Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarta maku cewa: ma'aikatar lafiya ta
Falasdinu a yau ranar Laraba a zirin Gaza ta sanar da cewa: Sojojin yahudawan
sahyoniya sun sake yin kisan kiyashi guda hudu kan fararen hula Palasdinawa a
cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Wannan ma'aikatar ta bayyana cewa: Falasdinawa 50 ne suka yi shahada sannan mutane 124 suka jikkata a wadannan hare-haren.
A cewar rahoton, adadin shahidan yakin da ake yi da Gaza ya karu zuwa mutane 40,223 sannan adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 92,981 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata wato 15 ga Mihr ranar da guguwar Al-Aqsa ta fara.
Sakamakon hare-haren da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai a wuraren zama, galibin shahidai da wadanda suka jikkata a yakin kisan kare dangi a Gaza mata ne da kananan yara.
Akwai dubban mutane ne da har yanzu ba a gansu ba ko sun kone ko suna a karkashin baraguzan da gininnikan da aka rusa a zirin Gaza.