Wasu 'yan kunar bakin wake hudu da ake kyatata zaton 'yan boko haram ne sun kai harin kunar bakin wake a wajen birnin Maiduguri na arewa maso gabashin Najeriya.
An kai harin ne a tashar motar Muna da ke kan hanyar Mafa-Dikwa,inda aka bayyana harin a matsayin mafi muni a jerin hare-haren da aka kai a cikin 'yan kwanakin nan cikin jihar ta Borno.
Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da dake hare-haren a tashar motar ta Muna, da ke kusa da sansanin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.
A ranar Litinin da ta gabata ma, an kai wani hari a jahar ta Borno, da ya hallaka mutane 9.