Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Shugaban yaɗa labarai na ƙungiyar Hashdush Sha'abi ta Iraki, yayin da yake nuni ga abubuwan da suka faru a wannan ƙasa a cikin shekaru ashirin da suka gabata, ya bayyana cewa, Iraki ta shafe zamuna na mamaya daga sojojin Amurka, Al-Qaida, da ISIL, kuma yanayin da ya mamaye ƙasar a lokuta daban-daban, ya samar da damar bullo da kasancewar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
"Muhand Al-Aqabi," a cikin hira da Al-Mayadeen, yana mai cewa, dole ne a bi da waɗannan batutuwa a cikin tsarin ilimi, ya ce: Wani lokaci muna ɗaukar wata ƙungiya mai ɗauke da makamai a matsayin jari na ƙasa, kuma wani ɓangare na bangaren gwagwarmaya.
Yana mai nuni ga yanayin al'ummar Shi'a ta Iraki kafin shekara ta 2003, ya kara da cewa: Al'ummar Shi'a a wancan lokacin tana fuskantar danniya, an mayar da ita gefe, ga mu'amala mai tsanani. Bayan shekara ta 2003 kuma, saboda mamayar Iraki da dakarun waje suka yi, wani ɓangare na wannan al'umma ya bi hanyar kishin ƙasa.
Al-Aqabi ya ci gaba da cewa, a biyo bayan waɗannan abubuwan, ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai sun bullo a tsakanin al'ummomi daban-daban na Iraki, ciki har da Shi'a; ƙungiyoyin da a yau ake kira su "ƙungiyoyin gwagwarmaya."
A cewarsa, ƙungiyoyin gwagwarmaya yanzu suna wani ɓangare na fagen siyasa da zamantakewa na Iraki, kuma an san asalinsu da sunayensu. Yawancin waɗannan ƙungiyoyi sun shiga tsarin siyasa, kuma wataƙila akwai ƙungiya ɗaya kawai da ba ta da kasancewar siyasa.
Ya bayyana cewa, dole ne a yi tattaunawa game da ƙungiyoyin da suka yi imani da wanzuwar makamai kawai, da kuma kiyaye su. Ya kara da cewa: Dukkan ƙungiyoyi suna da hedkwata a hukumance, jami'an tsaro suna da masaniya game da wanzuwar waɗannan hedkwatar, kuma ayyukansu a bayyane suke; don haka babu wata matsala ta musamman a wannan fanni.
Hashdush Sha'abi; Cibiya Ce Da Ta Fito Daga Gwagwarmaya
Al-Aqabi ya ci gaba da bayyana cewa, samuwar Hashdush Sha'abi ya samo asali ne daga fatawar babban malamin addini, Ayatullah Sayyid Ali Al-Sistani, kuma ya ce, ƙungiyoyin gwagwarmaya ne suka samar da tushe da ginshiƙi na farko na wannan ƙungiya.
Ya bayyana cewa, kafin fitar da wannan fatwa, ƙungiyoyin tsayin daka sun taru a gidan Haji Abu Mahdi Al-Muhandis, ɗaya daga cikin fitattun mutanen tsayin daka, kuma bayan wannan taro, aka fitar da fatawar marji’in addini.
Ya kara da cewa: Tushen samuwar Hashdush Sha'abi, ƙungiyoyin gwagwarmaya ne, kuma dukkan mutanen da suka kasance a matsayin kwamandoji a Hashdush Sha'abi, suna da alaƙa da ƙungiyoyin gwagwarmaya.
Al-Aqabi, yana mai jaddada wannan tarihi, ya ce, Hashdush Sha'abi ta fito daga cikin ƙungiyoyin gwagwarmaya, amma yanzu ta zama cibiya ta gwamnati, kuma tana bin umarni da ƙa'idojin hukuma.
Ya ci gaba da cewa: Yana da kyau a sami dokoki, kuma tsarin da cibiyoyin soji masu tsari, su yi aiki a ƙarƙashin tuta ɗaya da jagoranci ɗaya.
Wannan jami'in Iraki, game da matsayin Falih Al-Fayyad, shugaban ƙungiyar Hashdush Sha'abi, ya kuma ce, tun da daɗewa, har ma kafin kafa wannan ƙungiya, yana da dangantakar abokantaka da ƙungiyoyin gwagwarmaya.
Al-Aqabi ya bayyana cewa, Al-Fayyad ba shi da iko a kan ƙungiyoyin gwagwarmaya, Amma sashen da ya shafi Hashdush Sha'abi ne kawai ke ƙarƙashin umarninsa. A cewarsa, Al-Fayyad shine mutum na farko da ya sanar da sunan " Hashdush Sha'abi," kuma shi ne ya ɗauki alhakin shugabancin wannan ƙungiya.
Ya kara da cewa, Al-Fayyad wani muhimmin sashe ne na Hashd, kuma yana gudanar da ayyukan mutanen da suka dogara ga wannan ƙungiya.
Al-Aqabi, a lokaci guda, ya jaddada cewa, ƙungiyoyin gwagwarmaya suna da kwamandojinsu masu zaman kansu, kuma suna bin kwamandojin da suka shafe su. Ya ce: Muna da alhakin kare ƙasar da tsarin siyasa, kuma wannan shine mafi muhimmin tsari.
"Ba Mu Bin Wasu Mutane Na Musamman Ko Wata Hanya Ta Musamman"
Manajan yaɗa labarai na Hashdush Sha'abi, yana mai jaddada matsayin wannan ƙungiya a tsarin da ake ciki a yanzu, ya ce: Hashdush Sha'abi wani ɓangare ne na yanayin da ake ciki a Iraki, kuma tana aiwatar da duk wani mataki da ya dace da ƙasar. Ba mu bin wasu mutane na musamman, wata hanya ta musamman, ko wani yanayi na musamman ba.
Ya kuma sanar da cewa, Hashdush Sha'abi a yau tana fuskantar hari daga cibiyoyi masu gaba, waɗanda koyaushe suke ƙoƙarin kai hari ga kowane abu mai ƙarfi a Iraki.
Al-Aqabi, a martanin da ya mayar ga harin baya-bayan nan a kan hedkwatar Hashdush Sha'abi, ya ce: Wannan harin abin dariya ne; domin an bar mai kisan kai da ainihin laifin, kuma an mayar da muhawara ga bindiddigin bayanai game da ko Hashd ta san wannan batu ko batasani ba.
Ya kara da cewa: Koyaushe muna bayyana kanmu a matsayin ƙarfin tallafi da goyon baya ga sojoji da 'yan sanda.
Al-Aqabi, yana mai nuni ga tarihin Hashdush Sha'abi wajen fuskantar ta'addanci, ya ce: Mun sami nasarori. Mun kayar da ISIL, mun ba da shahidai da yawa, kuma an kashe yawancin kwamandojinmu.
Ya ci gaba da nuni ga damuwar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Iraki game da makomar kasancewar ɗayan bangare, kuma ya ce: Ƙungiyoyin da ke da makamai a Iraki, suna da damuwa game da ɗayan bangare; ciki har da yiwuwar ɗayan bangare ba zai fice daga Iraki ba.
Al-Aqabi ya kuma jaddada cewa, Satumba ba ranar ƙayyadaddiya ba ce, domin za a aiwatar da tsarin gudanarwa sannu a hankali.
Ba Za Mu Aiwatar Da Abin Da Amurka Ke Nema Ba
Shugaban yaɗa labarai na Hashdush Sha'abi, a wani ɓangare na maganganunsa, yana mai ƙin duk wani biyayya ga Amurka, ya ce: Mu ba jiha ko wani sashe na Amurka ba ne, kuma ba za mu aiwatar da abin da Amurka ke nema ba.
Ya kuma bayyana cewa, Iraki na iya taka rawa a cikin fahimtar juna da samar da kwanciyar hankali a yankin.
Al-Aqabi ya kara da cewa: Koyaushe muna sa ido kan yanayi, kuma koyaushe muna cikin babban matakin shiri. Wannan aikinmu ne, kuma muna aiki a cikin tsarin gwamnati da mulki.
A ƙarshe, yana mai nuni ga rawar Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen tabbatar da tsaron Iraki, ya bayyana cewa: Da ba Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, da babu tsaro a Iraki.
…………..
Ra'ayinka