Amurka Na Ci Gaba Da Kera Makaman Kakkabo Jigaren Marasa Matuka Na Iran A UAE

New York Times: Amurka Ta Kasa Magance Tasirin Jiragen Marasa Matuki Na Iran
23 Agusta 2026 - 21:45
Source: ABNA24
Amurka Na Ci Gaba Da Kera Makaman Kakkabo Jigaren Marasa Matuka Na Iran A UAE

Amurka da kawayenta, waɗanda suka kasa maganin jiragen marasa matuki na Iran, sun koma ga kamfanonin fasaha don samun hanyar fuskantar ƙananan jirage marasa matuki masu arha amma masu ƙarfi na Iran; Kamfanin Amurka "Powerus," tare da kafa kamfanin samarwa a UAE, yana kera kusan makamai masu kakkabo jirage marasa matuki 3,000 a kowane wata, kuma yana ƙoƙarin ƙara samarwa zuwa 15,000 a kowane wata a tsakiyar shekara ta 2027.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Kamfanin Amurka "Powerus," wanda ke da hedikwata a Florida, yana ƙoƙarin kera makamai masu linzami masu kakkabo jirage marsaa matuki masu arha don fuskantar jiragen marasa matuki na Iran. An kafa kamfanin samar da waɗannan makamai masu kakkabowa a UAE, kuma manufar kerarsu ita ce fuskantar jiragen marasa matuki na Iran masu sauri har zuwa mil 200 a cikin sa'a.

Mai magana da yawun wannan kamfanin makamai ya ce, masana'antar da ke da alaƙa da Powerus suna kera kusan 3,000 makaman kakkabo  jirage mara matuki a kowane wata, kuma kamfanin yana ƙoƙarin samar da cibiyar sadarwa na masana'antu wanda zai kai ya iya samar da makaman da yawan su ya kai 15,000 a kowane wata a duk faɗin duniya a tsakiyar shekara ta 2027.

Dangane da rahoton New York Times, kamfanin Powerus yana da niyyar biyan buƙatun gaggawa na ƙasashen da ke kawance da Amurka a yankin yammacin Asiya, kuma don wannan, ya fara haɗin gwiwa da masu samar da kayayyaki na gida a waɗannan ƙasashe, kuma yana gaggauta gina masana'antu don kera waɗannan na'urorin katsewa.

Ƙarfin jiragen marasa matuki na Iran ya tilasta wa kawayen yankin Amurka, ciki har da UAE, su gaggauta shirye-shiryen samar da na'urorin kakkabo jirage marasa matuki.

New York Times ta jaddada cewa, saboda raguwar yawan kayan yaƙi na Amurka, a yanzu kawayen wannan ƙasa suna buƙatar kera makamai masu linzami masu katsewa a cikin iyakokin su.

Yanzu, karancin kayan yaƙi na Amurka ya tilasta kamfanonin makamai su sauƙaƙe tsarin samar da kayan aikin soji da samar da kayayyaki tare da sauran kamfanoni. Samar da makamai masu arha na ɗaya daga cikin manyan damuwa na manyan kamfanonin soji na Amurka, don su rage kuɗin fuskantar makaman Iran. A gefe guda, Iran tana iya ƙalubalantar kayan aikin Amurka masu tsada da jirage mara matuki masu arha.

Powerus ba shine kawai kamfanin Amurka da ke kera na'urorin katsewa a UAE ba. A watan Oktoba, kamfanin Raytheon shima ya ba da rahoton shiga cikin kera makaman katsewa na "Coyote" a can.

Bisa ga wani rahoto daga Sabuwar Cibiyar Nazarin "Tsaron Amurka" a Washington, an ƙiyasta kuɗin kowane na'urar katsewa a dala 126,500.

Wasu kamfanonin fasaha kuma suna ƙoƙarin rage kuɗin samar da na'urorin katsewa. Misali, kamfanin fasaha "Neros" a Torrance, California, ya sanar da cewa yana haɓaka wata na'urar kakkabo jirgi maras matuki mai suna "Bandit," wanda nau'in farkonsa zai kai kusan dala 5,000.

…………..

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha