Jagoran ya bayyana haka a cikin jawabin bude taron da ya gabatar a taron kasa da kasa karo na 6 wanda aka bude a nan Tehra a yau Talata.
Aya. Khaminae ya bayyana cewa matsalar Palasdinawa ita ce matsalar da tafi ko wacce damun al-ummar musulmi, kuma ita ce sababin hada kan musulmi a abu guda.
Duk tare da bambance bambancen da al-ummar ta ke fama da su, wasun su su da kansu ne suka kirkiro rashin hadin kan, amma matsalar al-ummar Palasdinu wata matsala ce wacce zata hada kan Musulmi don kowa na da irin gudumawar zai zai bayar don ganin Palasdinawa sun sami nasara a kan HKI. Kuma banda musulmi ma sauran masu rajin kare hakkin bil'adama a ko ina suke a duniya indai da gaske suke Matsalar da al-ummar Palasdinu take ciki abin damuwa ne a garesu.288