7 Nuwamba 2026 - 21:50
Source: ABNA24
Tafarki Da Koyarwar Sayyidah Fatimah As A Musulunci

A zamanin da  da muke fama rikicewar ruwayoyi da Rashin ingancinsu da yadda raunin dangantakar ɗan adam da tushen ƙalubalen suka mamaye al'umma, sake karantawa da bitar tafarkin Sayyidah Fatimah Zahra (A.S) zai gabatar mana da bayyanannen hoton mace mai imani, mai sani, mai gina iyali kuma mai gina al'umma abar koyi da ke farawa daga gida har zuwa fagen bayyanawa, ilmantarwa da nauyin zamantakewa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA –: Sayyidah Shugabar Matan Duniya Da Lahira wadda ta gabatar da cikakken abin koyi na imani, ilimi, kasancewar zamantakewa, ɗaukar nauyi da kare gaskiya cikin sani. Rayuwarta gajeruwa amma mai albarka tana cike da koyarwa kan dangantakar addini, iyali, al'umma, mace, ɗabi'a da nauyin zamantakewa.

Daga cikin muhimman darussan da muka kowa daga gareta akwai bayyana gaskiya cikin sani, hidima ba tare da neman godiya ba, haɗa muhimmancin uwa da rawar zamantakewa, kula da maƙwabci da mabukata, da haɗa ƙauna da aikin da ita. Hudubarta shahararriya wadda ta fara da "Alhamdu lillahi ala ma an'am" wata fitacciyar misali ce ta balaga ta addini da kafa hujja a tarihin musulunci ba iya kare wani haƙƙi na kai ba kawai, said ai ta zamo misali mai ɗorewa na bayyana gaskiya daidai, mai dalili kuma cikin ƙarfin zuciya wajen fuskantar karkata da karkatarwa ga barin addini da wasu sukai.

Wannan hanyar ta ci gaba a koyarwar Ahlul-Bayt (A.S) daga hudubobin Amirul Muminin Ali (A.S) har zuwa kalaman Imam Hussein (A.S) a Karbala, hudubobin Sayyidah Zainab (A.S) a Kufa da Sham, da koyarwa da fadakarwar Imam Sajjad (A.S) da Imam Sadiq (A.S) wanda ya zama jigon kare akida da koyarwar Shi'a cikin tarihi.

A yau da mutane ke fuskantar tarin bayanai, ruwayoyi da nazari, ana buƙatar "bayyana gaskiya cikin adalci" fiye da kowane lokaci; domin zamanin bayanan sirri ba lalle ya zamo kamar zamanin fahimta ba. A bisa tsarida tafarkin Fatimiyya, bayyana gaskiya nauyi ne da ba ya takaita ga wata ƙungiya — kowane mumini mai sani zai iya ɗaukar matsayi bayyananne, daidai kuma na ɗabi'a a wajen fuskantar karkatarwa, rashin adalci da ɓata.

Har ila yau, tafiyarta tana gabatar da cikakken hoton asalin mace musulma inda uwa da mata da ibada da sanayya da nauyin zamantakewa da kare gaskiya suke samun ma'ana tare. Rayuwarta tana nuni da cewa mace musulma za ta iya kasancewa ginshiƙin kwanciyar hankalin iyali kuma a lokaci guda tana da tasiri cikin sani a fagen zamantakewa.

Labarin hadisin da ya shahara "Al-jaru summa al-dar" — "maƙwabci da farko, sannan gida" — yana nuni da zurfin hangen zamantakewa da ɗabi'arta har cikin addu'a da ibada. Kasancewarta a fagen zamantakewa tana nuni da cewa rawar iyali da mace kje takawa ba ta cin karo da ayyukanta na zamantakewa ba. Wannan tsarin ba ya kiran mace zuwa keɓewa da ficewa daga al'umma, kuma ba ya sadaukar da iyali don kasancewar zamantakewa.

A cikin wannan abin koyi, mace za ta iya kasancewa mai gina iyali kuma mai gina al'umma. A yau da wasu ƙungiyoyi ke mayar da mace kayan talla, wasu kuma suna gabatar da rawar iyali a matsayin cikas ga ci gaba, tsarin tafarkin Fatimiyya yana gabatar da daidaitacciyar hanya mai mutuntaka. A wannan mahangar, darajar mace ba ta cikin nunata cikin talla ba kuma ba ta cikin cireta daga fagen tasiri; a'a said ai tana cikin bunƙasa haƙiƙanin ɗan adam, imani, hankali, tsafta, tarbiyyar tsatso da shiga cikin al'umma bisa sanin nauyin da ya hau kai.

Mahangar Musulunci ga mace ta dogara kan darajar ɗan adam ta asali; a cikin wannan tsarin tunani, mace da namiji duka suna da damar girma, bauta, sani da tasiri. Mutane kamar Sayyidah Khadijah (A.S), Sayyidah Fatimah Zahra (A.S) da Sayyidah Zainab (A.S) bayyanannun misalai ne na wannan daraja da kwarewa.

Ana iya taƙaita muhimman sassan asalin mace a mahangar musulunci cikin wannan fannoni: imani, tsafta, hankali, tarbiyyar ɗan adam, gudanar da iyali, tasirin zamantakewa da kiyaye darajar ɗan adam. A bisa haka, mace ba wata halitta ta gefe ba ce a cikin al'umma kuma ba a bayyana ta cikin rawar da taka iya takawa a zahiri kawai ba; a'a said ai tana da rawar asali wajen gina iyali, al'adu da makomar al'umma.

Ɗaya daga cikin ƙalubalen yau shine tabarbarewar asalin mace musulma a cikin fagen watsa labarai da intanet. Kwatance akai-akai da abin koyi na kasashen waje, tallata salon rayuwa da ba su dace da darajar ɗan adam ba da matsayin al'adu, na iya sanya tunani da rayuwar mata da 'yan mata cikin shakku. Sake karantawa da bitar tafiya da tafarkin Sayyidah Zahra (A.S) na iya zama mafita a wannan fanni domin tana gabatar da daidaitaccen abin koyi na ruhi, sani da ilimi, daraja, kula da iyali da kasancewar zamantakewa.

Daga cikin muhimman sassan tafarkin da mahangar Fatimiyya akwai kula da nauyi da alhakin da doru akan mu’amala ta zamantakewa. Taimaka wa wasu a koyarwar addini ba ta iyakance ga taimakon kuɗi ba kawai; a'a taimakon tunani, goyon bayan zuciya, kiyaye mutuncin mumini, tare da mabukata da kula da matsalolin maƙwabci ma wani ɓangare ne na nauyin zamantakewar mumini. Sayyidah Zahra (A.S) kafin ta yi addu'a don kanta tana tunanin maƙwabta da wasu. Wannan mahangar yana nuni da al'ummar da mutane ba su nunawa juna rashin kulawa ba kuma dangantakar ɗan adam, ɗabi'a da zuciya tana raye tsakanin jama'a. A yau a yawancin al'ummomi musamman manyan biranen, dangantakar ɗan adam ta wargaje. Yawancin maƙwabta ba su san juna ba kuma dangantakar zuciya ta maye gurbinta da dangantaka maras karko ta aiki wani lokaci ta tattalin arziki kawai.

Sakamako kamar kaɗaici da kebance tsofaffi, raguwar amincewar zamantakewa da ƙaruwar rashin kulawa na jama'a, tushensu yana cikin wannan raunin haɗin kai. Tsari da tafarki koyarwa da mahangar Fatimiyya a wajen fuskantar wannan yanayi yana gabatar da wani nau'in cibiyar sadarwa mai rubanye uku na nauyi: na farko, nauyin gwamnati wajen samar da ayyukan jama'a da tallafawa sassan da suka fi rauni; na biyu, nauyin gamayya ta hanyar cibiyoyin jama'a, ƙungiyoyin sa kai da ƙungiyoyin agaji; na uku, nauyin da yahu kan mutum kowanne wajen taimakon kuɗi, tunani, zuciya da mutunci ga maƙwabci, mabukata da waɗanda ke killace.

Ƙauna ga Sayyidah Fatimah Zahra (A.S) ba iya ji ne a zuciya kawai ba, a'a dole ta kai ga sani, aiki da bin tafiyarta. Haɗin kai na gaskiya da ita yana samun ma'ana lokacin da mutum gwargwadon ƙarfinsa ya ɗauki salon rayuwarta, ɗabi'arta, imaninta, tsaftarta, nauyinta da neman haƙƙinta a matsayin abin binsa a aikace. Babban darasin rayuwarta ana iya taƙaita shi cikin ƙoƙari, bauta, rayuwa mai tsafta, sani, hidima, neman adalci da kula da zuciya.

Don haka, ƙauna ta gaskiya gare ta ba ta tsaya a ji da taken magana kawai ba, a'a tana samun ma'ana da tsaftar ciki, tuba da neman gafara, kula da wasu da nauyin aiki a wajen al'umma. Saboda haka, girmama Sayyidah Fatimah Zahra (A.S) ba ta taƙaita ga bayyana falalarta kawai ba, a'a tana buƙatar nazari, koyan darasi da sake karanta da bitar tafiyarta cikin amfani ga rayuwar yau; tafiyar da za ta iya zama bayyanannen jagora da abin ƙarfafa zuciya a fannin iyali, watsa labarai, ɗabi'ar zamantakewa, asalin mace da nauyin jama'a.

Marubuciya: Zainab Khatoon Shirinkar

Madogara:

1. Sheikh Sadouq, Ilal al-Sharai', 1966, Juzu'i na 1, Shafi na 182.

…………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha