Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Abubuwan da suka faru na tsaro na baya-bayan nan a yammacin Asiya da rashin ikon Amurka na hana faɗaɗa rikici da gazawarta wajen dakile kowane hari dga Iran da ke sauka kan sansanonita da ma kayayyakin more rayuwar kasashen da ta ke acikinsu, sun sa wasu kasashen Larabawa na Tekun Farisa neman sake fasalin ma'aunin tsaronsu da samun sabbin abokan tsaro.
A cikin wannan tsugugi, rahotannin da aka buga game da tattaunawar tsaro tsakanin Pakistan da kasashen Larabawa sun nuna cewa Kuwait, Bahrain da Jordan suna neman haɓaka hadin gwiwar soji da Islamabad; tsarin da masu sa ido da yawa ke ɗauka a matsayin alamar raguwar amincewa da tsarin tsaro na gargajiya na Amurka.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters a cikin wani rahoto ya bayyana cewa Pakistan da Kuwait sun fara tattaunawa don haɓaka hadin gwiwar tsaro, kuma Kuwait ta buƙaci kasancewa da hadin gwiwar soji mai faɗi da Islamabad. Wannan rahoto ya kuma jaddada cewa Bahrain da Jordan ma sun nuna sha'awar yarjejeniya irin wannan da Pakistan.
Waɗannan motsi suna faruwa ne a daidai lokacin da a cikin 'yan watannin da suka gabata, sansanoni da muradun Amurka a yankin suka sha fuskantar barazana da hare-hare, har ma wasu kasashen Larabawa ciki har da Bahrain, Kuwait da Jordan, a cikin tashin hankalin da ke da alaƙa da arangamar Iran da Amurka, sun tsinci kansu cikin hadari kai tsaye. A lokaci guda, ƙaruwar damuwa game da tsaron muhimman ababen more rayuwa na kasashen Tekun Farisa da yiwuwar faɗaɗa rikici, sun ƙara shakku game da ƙarfin fifikon yaƙin Amurka.
A cikin irin wannan yanayi, Pakistan a matsayin ƙasa mai ƙarfin nukiliya mai manyan sojoji, ƙarfin makamai masu linzami da masana'antar tsaro mai mahimmanci, ta zama abin sha'awa ga gwamnatocin Larabawa fiye da dā. Reuters ta ba da rahoton cewa bayan sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakanin Riyadh da Islamabad, wasu kasashen Larabawa da dama su ma sun tuntuɓi Pakistan don irin wannan haɗin gwiwa.
Tun da farko Saudi Arabiya ta kuma sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro ta dabaru da Pakistan, wadda bisa gare ta, dubban sojoji, jiragen yaƙi na JF-17, jirage mara matuki da tsarin tsaro na Pakistan aka girka a ƙasar Saudiyya. Masu sa ido sun yi imanin cewa karɓar da kasashen Larabawa suke yi wa tsarin haɗin gwiwa da Pakistan, ba shawara ce ta soji kawai ba, a'a, alama ce ta canji a hankali a ra'ayin tsaro na yanki da ƙoƙarin rage dogaro da Amurka gaba ɗaya.
Wasu manazarta sun yi imanin cewa tattaunawar tsaro ta baya-bayan nan tsakanin Pakistan da kasashen Larabawa na iya zama ɗaya daga cikin alamomin farko na samuwar sabbin shirye-shiryen tsaro a yankin; shirye-shiryen da a cikinsu gwamnatocin Larabawa ke neman bambanta abokan tsaronsu, kuma ba su dogara ga garantin sojin Washington kawai ba.
Wanda Amurka Ta Kasa Karewa Ina Wata Pakistan Zata Iya Karewa??
Menene Ra’yinku Akai!?
…………….
Ra'ayinka