Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ofishin Hulda da Jama'a na Dakarun Juyin Musulunci na Iran a cikin sanarwa mai lamba 19 na aikin Nasr 2, da lambar sirri mai albarka ta "Ya Aba Abdillahil Husain (A.S)," sun kawo cewa:
A martani ga munanan ayyukan sojojin Amurka makisa yara, mayakan rundunar sararin samaniya na dakarun juyin musulunci, a zagaye na goma sha ɗaya na aikin Nasr 2, da lambar sirri mai albarka ta "Ya Aba Abdillahil-Husain (A.S sun kai harin bazata a kan cibiyar kwamandancin ayyuka na musamman na makiya a yankin Al-Tanf na Siriya, baya ga lalata wata na'urar radar, da jirage masu saukar ungulu na ayyuka na musamman, a matsayin ramuwa ga jinin sojojin shahidan na daren jiya a Iran shahr, dimbin sojojin Amurka masu laifi suka sheka a harin.
Sun kara da cew: Cikakken ikon sarrafa mashigar Hurmuz har yanzu yana hannun jaruman mayakanmu, kuma matuƙar munanan ayyukan Amurka suka ci gaba, ba za a fitar da ko digo ɗaya na man fetur da iskar gas daga wannan yanki ba
Kuma Babu Wata Nasara Fa Ce Daga Wurin Allah Mabuwayi Mai Hikima.
………………………
Ra'ayinka