16 Yuli 2026 - 14:53
Source: ABNA24
Hedkwatar Khatam: Idan Ku Harbi Ababen More Rayuwarmu, Duk Abubuwan More Rayuwa Da Ya Rage A Yankin Za Mu Kai Masu Hari

Mai Magana Da Yawun Hedikwatar Tsakiya Ta Khatam Al-Anbiya A Cikin Wani Gargadi Ga Makiya Ya Bayyana: Idan Ku Harbi Ababen More Rayuwarmu, Duk Abubuwan More Rayuwa Da Ya Rage A Yankin Za Mu Kai Masu Hari

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Kanar Ebrahim Zolfakhari, mai magana da yawun hedikwatar tsakiya ta Khatamul-Anbiya, a cikin wani gargadi ga makiya ya bayyana: Idan ku harbi ababen more rayuwarmu, duk abubuwan more rayuwa da ya rage a yankin za mu kai masu hari

Cikakken bayanan sun zo kamar haka:

‘Yar Ta’addar Amurka, tana ci gaba da tayar da zaune tsaye da rashin tsaro a yankin.

Da farko, muna sake jaddada cewa, a kowane hali kuma ta kowace hanya, ba za mu bar Amurka a matsayin wata ƙasa ta waje ta wajen yankin ta tsoma baki a mashigar Hurmuz ba. Wannan shine jan layin Iran da ba za’a iya tsallake shi ba.

Idan barazanar baya-bayan nan na shugaban Amurka, wacce take cike da wofanci, game da kai hari a kan ababen more rayuwa na Iran din Musulunci da sojojin mamaya na wannan ƙasa ta faru, to duk abin da, saboda mutuncin Iran, ya rage lafiya lau - wato dukkan ababen more rayuwa a yankin - za su sha murkusa su da manyan hare-hare na ƙarfin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran; ta yadda babu wata alama da za ta rage gare su, kamar dai ba su taɓa wanzuwa ba tun farko.

Makiya jahilai su sani: Lokacin jarumtaka a gare mu, ba lokacin takatsantsan ba ne. Abin da ke faruwa daga sojojin Iran, ba harin daidai da daidai ba ne, hari ne mafi ƙarfi. Hare-haren da za su yi tsanani, faɗaɗa da kuma halakarwa fiye da kowane lokaci. Wutar fushin al'ummar da ba ta taɓa mika wuya ba, za ta kona masu mamaya.

Kuma Dukkan Wata Nasara Kawai Daga Allah Maɗaukaki Mai Hikima Ce.

………

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha