Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya kawo maku cikakkiyar fassarar sakon jagoran juyin juya halin musulunci. An wallafa saƙon Jagoran Juyin Juya Hali dangane da gagarumin lamarin rakiyar gawar “Shahidin Iran” da bayanin muhimman batutuwan ƙasar.
Ga Fassarar Cikakken Saƙon Ayatullahi-Uzma Sayyid Mujtaba Khamene'i Kamar Haka:
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.
Ya Ku Al'ummar Iran Masu Girma Da Ban Al'ajabi!
Aminci da gaisuwa da godiya su tabbata a gare ku, ku da kuka tabbatar da wata gagarumar bajinta ta musamman kuma ta tarihi, a cikin wannan babban yunkuri da ba a taɓa ganin irinsa ba na rakiyar Shahidin Iran, inda kuka kafa sabon ma'auni na bayyana ruhin tayar da al'umma da kuma ƙudurin ainihin asalin Musulunci da na Iran wajen sanin girma, da sallamawa, da basira, da nuna ƙauna ta musamman ga jagoran al'ummar Musulunci da shahidin juyin juya hali.
Zafin zukatan da suka narke, idanun da suka cika da hawaye, da ƙuduri mai ƙarfi na taron miliyoyin jama'a da suka bayyana a tsawon kilomitoci da dama a Tehran, Qum, Mashhad da sauran birane da ƙauyuka, sun sanya abokan al'ummar Iran da 'yantattun mutanen duniya abin yabawa, yayin da suka jefa maƙiya masu girman kai na al'ummar Iran cikin ruɗani, da fushi da tsoro.
A lokaci guda da wannan bajinta, maimaita karya alkawurran Babban Shaidan dangane da yarjejeniyar fahimtar juna da shugabannin ƙasashen Iran da Amurka suka sanya wa hannu, ya sake tabbatar wa kowa wannan gaskiya cewa sa hannun shugaban ƙasar Amurka ba shi da wata ƙima kuma ba abin dogaro ba ne, kuma zalunci, son mallake komai da kuma dabbanci sassa ne da ba za su rabu da dabi'ar Amurka ba.
A yau, Babban Shaidan ya sake bayyana ainihin fuskarsa ba tare da abin rufe fuska ba, domin wannan mummunar ƙwarewa mai cike da duhu ta ta’addanci da karya alkawari ta zama wata hujja mai ƙarfi ta ƙarya, rashin hankali, rashin amana da muguntar Amurka.
Yanzu da maƙiyiya Amurka ke neman rura wutar yaƙi tare da ɗaukar ƙarin nauyin asara da kuma ƙara kunyata kanta, ta sani cewa al'umma mai daraja ta Iran da kuma kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci suna da darussa da ba za a taɓa mantawa ba gare ta; jarumtakar mayaƙan gwagwarmaya da kuma ƙwazon mutanen jaruman yankin kudu a cikin waɗannan kwanaki sun nuna wasu misalai daga cikinsu.
Ya dace in fada ma ku, ku al'umma masu aminci da ɗaukaka ta Iran, cewa daga cikin mafi muhimmancin al'amura a wannan lokaci akwai dagewa kan haɗin kai a dukkan matakan jama'a da jami'ai, da a dukkan fannoni domin cimma manyan manufofin Juyin Juya Halin Musulunci da tabbatar da ɗaukaka da 'yancin kai na Iran mai daraja, musamman a wajen fuskantar yar ta’addar maƙiyiya da makirci ta Amurka.
Kamar yadda aka yi ta tunasarwa akai-akai da jaddadawa tun da farko, kiyaye haɗin kai da kauce wa rarrabuwar kai da rikici, da sabanin siyasa da kuma fito da bambance-bambancen zamantakewa, nauyi ne na kowa da kowa. Kuma hakika rawar da jami'ai da masu kishin juyin juya hali da Imam da Shahidin jagora ke takawa wajen tabbatar da haɗin kai da dunkulewar ƙasa ta fi muhimmanci kuma ta fi sarkakiya.
Bisa wannan, al'umma mai daraja, tare da ci gaba da amincewa da jami'ai masu kishin al'umma a dukkan ɓangarori uku na gwamnati, waɗanda ƙoƙarinsu wajen samar da walwala da jin daɗin al'umma yake a bayyane, za ta ci gaba da kasancewa cikin faɗakarwa da aiki a fagen kare muradun Iran ta Musulunci.
Mai yiwuwa wasu mutane da ke da cikakken ikhlasi da niyyar alheri su kasance suna da wasu suka ga ayyukan wasu jami'ai. A ganina, duk da cewa wannan damuwa da kulawarsu ga tsarin Musulunci wata babbar kadara ce mai daraja kuma a kashin kanta abu ne abin so, waɗannan masoya, waɗanda wasu daga cikinsu suna daga cikin jagorori masu basira, dole ne su kula kada wannan salon sukar ya zama, na farko, zalunci ga wani maras laifi, domin hakan kansa yana zama sanadin hana samun albarka da kulawa daga Allah. Na biyu kuma, kada ya zama sanadin karya haɗin kai da dunkulewar al'umma; domin idan aka kiyaye waɗannan sharuɗɗa, suka za ta zama sanadin bunƙasa da ci gaban al'amura.
Kada maƙiyi ya ga wata alamar rauni daga gare mu, har da irin wannan raunin; domin duk lokacin da muka kiyaye waɗannan abubuwa gaba ɗaya, babu makawa zai juya baya cikin shan kaye.
Ina sake miƙa godiya ta daga zuciya ga kowane ɗan ƙasa mai daraja, waɗanda su kansu masu makokin shahidi uban al'umma ne, kuma duk da wahalhalu da wasu ƙuntatawa da rashin jin daɗi, suka ƙirƙiri wata bajinta ta tarihi a wannan gagarumin al'amari na rakiyar Shahidin Iran.
Haka kuma ina gode wa manyan Maraji'an Taqlid, malamai, masu Tunani da fitattun masana, masu fafutukar al'adu, zamantakewa da siyasa, da kuma kokari da ayyukan cibiyoyin ƙasa da na soji, tare da halartar manyan jami'ai da wakilan kungiyoyin gwagwarmaya mai ɗaukaka da kuma ƙungiyoyin Musulunci ababen alfahari.
Ina fatan duk waɗanda suka halarta, suka raka, ko suka nuna goyon baya da haɗin kai ta kowace hanya a cikin wannan bajinta ta tarihi, su kasance cikin kulawa da addu'a ta musamman daga Ubangidanmu, Allah Ya gaggauta bayyanarsa.
Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i
26 ga Tir 1405 (18 ga Yuli 2026)
........................
Ra'ayinka