Domin samar da hanyar sadarwa tsakanin daliban Ghana da suka kammala karatun jami'o'in Iran da kuma amfani da karfin gida wajen raya alakar Tehran da Accra, an kafa cibiyar kungiyar al'adu ta Iran a Ghana.
Kasashen Iran da Rasha sun fara hadin gwiwa don gano albarkatun lithium a Iran. Ya zuwa yanzu, an gano adadin wannan karafa a cikin lardunan Qum, Isfahan, da Semnan. Kwararru na Rasha da manyan dakunan gwaje-gwaje na kasar su ma sun shiga cikin wadannan binciken.