Jordan 1
-
Al’ummar Jordan Sun Sanya Hannu A Wasikar Buɗaɗɗiya A Don Korar Sojojin Amurka
Daruruwan jiga-jigan siyasa, shari'a, da na jama'a na Jordan sun sanya hannu a wata buɗaɗɗiyar wasika inda suka buƙaci korar sojojin Amurka daga ƙasar.
-
IRGC: Mun Lalata Na’urar Tsaron Sama Ta Patriot Da Na’urar Leken Asiri A Arbil
IRGC: Sojoji Da Dama Sun Sheka Da Raunatar Wasu A Mummmunan Hari Kan Sansanin Amurka A Al-Azraq A Jordan
Dakarun Juyin Musulunci na Iran: Mun kai hari mai halakarwa a kan sansanin Amurka a Al-Azraq a Jordan, mun lalata na’urar tsaron sama nau'in Patriot da balloon na leken asiri a Arbil. Amurka mai kashe yara yana ƙarya a fili ga al'ummarsa da sauran mutane game da adadin wadanda suka mutu, kuma muna kira ga cibiyoyin bincike da kafofin yada labarai da su gudanar da bincike a fagen game da wannan.
-
Ba'amurken Marubuci: Trump Ya Mai Da Rayukan Sojojin Amurka Sadaukarwa A Yaƙin Sa Kai
Wani marubuci kuma manazarcin Amurka, yana mai sukar aikin Donald Trump a yaƙi da Iran, ya jaddada cewa shugaban Amurka har yanzu bai bayar da cikakken bayani game da manufofin wannan yaƙi da dalilin mutuwar sojojin Amurka ba, kuma ya jefa rayukan sojojin wannan ƙasa cikin hadarin "yaƙin d ya sa kansa."
-
Iran Ta Daidaita Makamanta Da Na’urorin Tsaron Amurka
Iran Tana Amfani Da Makamai Masu Linzami Masu Sauri Da Ƙarfin Motsi
Jaridar Wall Street Journal, ta nakalto daga jami'an Amurka, rahoton cewa Iran, ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu sauri da ƙarfin motsi, ta daidaita da tsarin na’urorin tsaron Amurka. An buga wannan rahoto ne a daidai lokacin da jami'an Amurka da sojojin wannan ƙasa da dama suka jikkata a hare-haren Iran na baya-bayan nan a kan sansanonin Amurka a Jordan, kuma sojoji biyu sun mutu. Hotunan tauraron dan adam sun tabbatar da lalata rumfunan shirya jiragen yaƙi a sansanin Muwaffaq al-Salti.
-
Cikakken Bayani Game Da Hare-Haren Iran A Kan Sansanin Sojojin Amurka A Jordan
Jaridar New York Times, ta nakalto daga jami'an Amurka, ta ba da rahoton cewa harin Iran na ranar Juma'a, shi ne hari na huɗu a cikin kwanaki biyar da suka gabata wanda ya kai hari kan sojojin Amurka a Jordan.
-
Raunin Amurka A Yankin; Kuwait, Bahrain Da Jordan Sun Garzaya Neman Na’urar Tsaron Pakistan
Manazarta sun yi imanin cewa tattaunawar tsaro ta baya-bayan nan tsakanin Pakistan da kasashen Larabawa na iya zama ɗaya daga cikin alamomin farko na samuwar sabbin shirye-shiryen tsaro a yankin; shirye-shiryen da a cikinsu gwamnatocin Larabawa ke neman bambanta abokan tsaronsu, ba su dogara ga garantin soji na Washington kawai ba.
-
Iran; Ta Aike Da Sako Ga Al'ummar Jordan
Iran: Ta Kai Hari A Kan Cibiyar Umarni Da Sarrafawa Ta Amurka A Jordan
Rundunar sararin samaniya ta dakarun juyin musulunci ta kai hari a kan sansanin Al-Azraq na Jordan da makamai masu linzami na "Khaibar Shikan," kuma ta yi kira ga al'ummar Jordan da su kai hari ga muradun Amurka yar mamaya su tsarkake ƙasarsu daga gare su.
-
IRGC: Sun Baje Cibiyar Kwamandancin Amurka A Yammacin Asiya Da Sansanin Sojan Sama Na Al-Azraq Na Jordan
Dakarun Juyin Musulunci na Iran a cikin wata sanarwa sun ba da rahoton murkushe cibiyar kwamandanci da sarrafawar makiya a Yammacin Asiya da sansanin sojan sama na makiya a Al-Azraq na Jordan da makamai masu linzami na ballastic guda 10.