Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Filin Sab'in a Sana'a ya shaida muzaharar miliyoyin al’umma, haka kuma jama'a da ba a taɓa ganin irinsu ba sun kwarara zuwa ɗaruruwan filaye a larduna da dama na Yemen, a ƙarƙashin taken "Juma'ar Gargadi Da Yunkuri.
Babban Shugaban majalisar siyasa, Mahdi Al-Mashat, ya ce: "Lokacin da shugaban ƙungiyar Ansarullah, Sayyid Abdul-Malik Al-Houthi, ya yi gargadi, kuma al’ummar Yemen masu imani da hikima ta amsa masa, to ku daidaita agogonku da lokacin Sana'a".
Ya kara da cewa, a wannan lokaci: "A gaban haƙƙoƙin halal da buƙatun gaskiya, ƙalubale suna faɗuwa; ko dai haƙƙoƙi ga kowa, ko kuma babu haƙƙi ga kowa."
Shugaban majalisar siyasa mafi girma, Mahdi Al-Mashat: Lokacin da Sayyid Al-Houthi ya yi gargadi, kuma Yemen na imani da hikima ta amsa masa, to ku daidaita agogonku da lokacin Sana'a.
Ya kara da cewa: "A gaban halastattun haƙƙoƙin da buƙatun gaskiya dukkan ƙalubale suke saraya; ko dai samar da haƙƙoƙi ga kowa, ko kuma ya zamo kowa ya rasa haƙƙinsa".
A nasa bangaren, shugaban ƙungiyar malaman Yemen, Sheikh Shamsuddin Sharafuddin, ya sanar da sallamwa da ba wa shugaban ƙungiyar Ansarullah, Sayyid Abdul-Malik Al-Houthi, wuka da nama wajen ikon ɗaukar dukkan qudurori masu dacewa don kare ƙasar.
"Muna sanar da salamwarmu ga Sayyid Abdul-Malik Al-Houthi don ɗaukar dukkan shawarwarin da suka dace don kare ƙasarmu."
Sharafuddin ya jaddada "Kara bar makiya su cimma abin da suka shirya," yana mai nuni da cewa a dauki "Killacewar a matsayin yaƙi kawai".
Za Mu Ɗauki Duk Wata Killacewar A Matsayin Yaƙi.
Sharafuddin ya kira sojojin Yemen: Muna kira ga sojojinmu da su ɗaga matakin martani, kuma muna kan mafi girman shiri don tallafa wa fagage.
Sharafuddin ya jaddada matsayin Yemen: "Muna jaddada matsayinmu na tsayayye game da batun Falasdinu da tsayawarmu tare da Hizbullah da Jamhuriyar Musulunci a Iran."
Yemen Na Fuskantar Ta'addancin Saudiyya
"Juma'ar Gargadi Da Yunkuri" ta zo ne bayan ta'addancin Saudiyya a kan filin jirgin sama na Sana'a, kuma sojojin Yemen sun mayar da martani ta hanyar kai hari a kan filin jirgin sama na Abha a cikin Saudiyya.
A cikin tsarin ma'aunin fage, sojojin Yemen sun yi gargadi ga dukkan kamfanonin jiragen sama da su guji wucewa a sararin Saudiyya, suna kira gare su da su "ɗauki gargadinmu da muhimmanci har sai an ɗaga killacewar filin jirgin sama na Sana'a".
Sayyid AlHouthi ya jaddada, a cikin jawabinsa na jiya Alhamis, cewa "Yemen za ta mayar da martani daidai da daidai, killacewa da killacewa, idan Saudiyya ta nufi tashin hankali gaba ɗaya".
Sayyid Al-Houthi ya yi gargadin cewa "dukkan cibiyoyin man fetur da wurare masu muhimmanci na Saudiyya sune manufa ga makamai masu linzami da jirage mara matuki na Yemen idan ta shiga cikin ta'addanci a kan ƙasarmu".
………….
Ra'ayinka