18 Yuli 2026 - 23:38
Source: ABNA24
Pezeshkian: Sakon Hikima Da Haɗin Kai Na Jagora Shine Mafi Muhimmancin Kariya Ga Muradun Kasa

Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya ɗauki sako mai cike da hikima da haɗin kai na jagora mai girma na juyin juya halin Musulunci a matsayin mafi muhimmanci ga kare muradun kasa da ci gaban Iran Musulunci.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Shugaba Masoud Pezeshkian a yau Asabar da dare  18 Yuli, 2026, a shafin sada zumunta na X ya rubuta: Sako mai cike da hikima da haɗin kai na jagora mai girma na juyin juya halin Musulunci da goyon bayansa ga shugabannin rassa uku da jami'an ƙasar, shine kariya mafi muhimmanci ga muradun kasa da ci gaban Iran Musulunci.

Shugaban kasa ya kara da cewa: Tabbatuwa ga bin abubuwan da suka shafi hadin kai mai tsarki da guje wa sabani da rarrabuwa, shine asalin nasara a wannan lokaci mai muhimmanci.

………………….

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha