Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa Ahlul Bayt (as) - ABNA - ya habarta cewa: a daren ranar Asabar din jiya ne jiragen yakin Amurka suka kai hari a yankunan Al-Sauma’a, Al-Salem da Al-Munirah da ke tsakiyar kasar Yemen da arewaci da kuma yammacin kasar.
Jiragen yakin Amurka sun kai hari a wata kwalejin koyon sana'a da ke yankin Al-Sauma'a da ke gabashin gundumar Al-bayda da ke tsakiyar kasar Yemen sau 5.
A halin da ake ciki kuma an kai hare-hare uku a yankin Sahlin da ke gundumar Al Salem na yankin Kataf a gabashin lardin Sa'ada a arewacin kasar Yemen.
Hakazalika jiragen yakin Amurka sun kai hari a yankin Al-Munaira da ke arewa maso yammacin lardin Al-Hodeidah a yammacin kasar Yemen da hare-hare guda biyu.
Ya kamata a lura da cewa, a ranar 15 ga Maris 2025, Amurka da Birtaniyya tare da goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan sun kaddamar da hare-hare ta sama kan kasar Yaman, inda suka auna wuraren zama da cibiyoyin fararen hula a kasar.
Your Comment