Hizbullah Ta Ƙi Amincewa Da Miƙa Makamanta Ako Wane Yanayi 

Hizbullah Ta Kafe Kan Kiyaye Makamanta Duk Da Matsin Lamba
25 Oktoba 2025 - 21:11
Source: ABNA24
Hizbullah Ta Ƙi Amincewa Da Miƙa Makamanta Ako Wane Yanayi 

Yayin da Ministan Harkokin Wajen Lebanon ya sanar da cewa "girman barnar da aka yi a kudancin kasar ya kara mana kudirin takaita makamai a hannun gwamnati," Hezbollah ta dage kan matsayinta na baya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: "Mahmoud Qamati" Mataimakin Shugaban Majalisar Siyasa ta Hezbollah, ya jaddada a yau (Asabar): "Wannan kungiya ba za ta taba mika makamanta ba, domin makiyiyarta Isra'ila tana kai mana hari a kowace rana, kuma babu wani matsin lamba daga Amurka da Turai da zai iya dawo da mu daga tafarkin gwagwarmaya".

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha