25 Oktoba 2025 - 20:29
Source: ABNA24
Amurkawa Sun Mayar Da Martani Ga Rubutun Trump Na Izgilanci + Hotuna

Bayan Trump ya saka wani bidiyo da aka nuna yana jefa sharar kazanta ga masu zanga-zangar Amurkawa, wasu masu fafutukar Amurkawa sun mayar da martani ga sakonsa mai cike da izgili.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Labarai da yawa sun bayyana game da miliyoyin Amurkawa da sukai zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Amurka. Suna rera "Bama yin mulkin sarauta, bama yin kanben sarauta, bama yin sarakuna," mutane miliyan bakwai sun fito kan tituna suna adawa da dimokuradiyyar Amurka ta kama karya. Duk da haka, martanin Trump ga zanga-zangar jama'ar Amurka ya haifar da ce-ce-ku-ce mai yawa.

Masu amfani da kafafen sada zumnuta na Amurkawa sun maida martani ga irin wannan martani na rubutun da Trump ya watsa yana mai masu izilanci

Shugaban Amurka ya saka wani bidiyo da aka samar ta hanyar AI a shafinsa na sada zumunta wanda ke nuna shi yana amfani da jirgin yaki don jefa shara ga masu zanga-zangar Amurkawa da ke zanga-zanga a titunan Amurka.

Daruruwan zanga-zanga a daruruwan biranen Amurka, ciki har da Los Angeles, New York, Washington, Chicago, Miami, Boston, Seattle, Atlanta, da Austin, sun jawo hankalin jama'a da yawa. Babban taken shine "Bama yin Sarki," wanda suka yi amfani da shi azaman suka ga manufofin mulkin kama karya na Shugaba Donald Trump.

Bidiyon Trump da aka samar ta hanyar AI, wanda ya wulakanta al'ummar Amurka a fili, ya haifar da fushi mai yawa a tsakanin jama'ar Amurka, kuma masu amfani da kafofin sadarwa na Amurkawa sun nuna fushinsu da bacin ransu a shafukan sada zumunta. Wasu masu amfani sun mayar wa Trump martani ta hanyarsa—"mayar da martani ta hanyar iri ɗaya"—har ma sun ninka sama da haka. Yanzu, wannan nuna halin ƙiyayya da Trump ya yi ya zama babbar matsala a gare su.

Wasu masu suka sun mayar wa Trump martani ta hanyar da yayi anfani da ita wato zanya hotunan izgili, kuma hashtag "#TrumpSmells" ya zama babban batu a shafukan sada zumunta, inda suke yada hotunansa cikin kaskantawa da wulakantawa.

Tun da farko, wasu masu amfani sun buga hotuna da ke nuna kazanta a fuskar Trump da taimakon fasahar kere-kere ta Ai, don mayar da martani ga cin zarafin Trump ga masu zanga-zangar Amurka.

Masu suka sun yi gargadin cewa wasu daga cikin ayyukan gwamnatin Trump ba su dace da kundin tsarin mulkin kasar ba kuma suna barazana ga 'yancin fadin albarkacin baki da dimokuradiyya a Amurka. Matakin Trump ya nuna ra’ayinsa ga zanga-zangar ta hanyar cin mutunci ga jama'ar Amurka.

Masu fafutuka a kafofin sada zumunta sun ce Trump zai fuskanci mummunan sakamako saboda ayyukansa. Ba zai iya mayar da martani ta wannan hanyar ga taron masu suka ba, miliyan bakwai daga cikinsu sun fito kan tituna su kaɗai, kuma bai bayar da wani martani mai mahimmanci ba.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha