Kamfanin dillancin labarain kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Alexander Turbanov fursunan da dakarun Hamas suka saki a musayar fursunonin da aka yi a kwanakin; ya bayyana godiyar sa ga dakarun yadda suka kula da shi da sauran fursunonin cikin aminci.
Ya ci gaba da bayyana nagartar halayen dakarun Hamas da ya gani, a yayin da yake musu godiya yana mai cewa: “Duk da zalunci wahalhalun da kuka sha amma kun gina alherinku cikin zuciyata na har abada...”
Na dauki kwanaki 600 a tsakanin ku... duk da hare-hare da kisan gillar da kuka sha, na koyi ma’anar riƙo da gaskiyar jarumta, da girmama ɗan Adam da dabi’u masu kyau...
Ku ne 'yan ƙasa masu 'yanci da aka kewaye da duhu, ni kuwa a matsayin fursuna... ku ne kuka tsare rayuwata... kuka kula da ni kamar yadda uba mai ƙauna ke kula da yaransa... kuka kiyaye lafiyata, mutuncina da walwalata...
Ko da yake na kasance a hannun mazan da ke yaƙi don ƙasarsu da haƙƙinsu da aka kwace, duk da cewa Hukumar Isra'ila na aikata mummunan kisan ƙare dangi kan al'ummarku wacce ke cikin matsanancin Talauci, duk da haka ba ku taɓa barina na ji yunwa ko cin mutunci ba.
Ban san ma’anar gwarzontaka ta gaskiya ba sai da na gan ta a idanuwanku... ban fahimci sadaukarwa ba sai da na rayu tare da ku... Mafiya yawan lokaci na ga kuna murmushi duk da barazanar mutuwa da ake muku da ma kisan ƙare dangi da kuke fuskanta.
Kuna gwagwarmaya da wani maƙiyi da ke da makaman hallakarwa tattare da goyon bayan kasashen masu cin zali da mamaya, amma babu abin da kuke da shi sai jikinku da imani... ba zan taɓa samun kalmomin da za su bayyana darajarku ba... Ko yadda nake mamakin halayyarku mai daraja ba...
Shin Addininku Yana Koya Muku Ku Kula Da Fursunoni Haka Ne?
Gaskiya, wannan imani naku yana ɗaukaka ku zuwa wani matsayi da duk dokokin da ɗan adam ya kafa kan 'yancin ɗan adam da dokokin yaƙi ke fāɗuwa gabansa...
Ko da a cikin mawuyacin hali, kuna bayyana adalci da jin ƙai... ba kawai a cikin maganganu marasa amfani ba, sai dai a cikin aikace-aikacen rayuwarku... ba ku bar dabi’unku nagari ba ko da a cikin duhun fitintinu da far gaba.
Da za ku yarda da ni, idan har na dawo nan, ba zan zama komai ba face dalibin mujahidi a cikin sahun ku... domin na koyi gaskiya daga al’ummarku... kuma na fahimci cewa ba kawai ku ne masu wannan ƙasa ba — ku ne masu ɗabi’u da shari’ar gaskiya...
Haj EMAAD
Your Comment