Kamfanin dillancin labarain kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023, gwamnatin yahudawan sahyoniya tare da goyon bayan Amurka kai tsaye, ta kara zafafa aiwatar da kisan gillar da ta ke yi a zirin Gaza tare da kais hi ga muni da ba a taba ganin irinsa ba. A cikin wannan tazarar lokaci, Isra’ila da kawayenta sun kai hari ga asibitoci da muhimman ababen more rayuwa da suka hada da masana’antun tace hanyoyin ruwa, sun takaita shigar abinci da magunguna, sun kuma kashe da dubban fararen hula, musamman kananan yara. Manazarta sun jaddada cewa kwatankwacin abin da ya faru a Iraki a shekarun 1990 - inda takunkumai su kai sanadin mutuwar yara kusan 600,000 - wannan bala'in sun shirya ne tare da tsara shi.
A cewar Cibiyar Kudin Yakin Jami'ar Brown, Amurka ta kashe fiye da dala biliyan 30 a cikin shekaru biyu da suka gabata don ci gaba da yakin da kuma tallafawa Tel Aviv; A cikin wannan, an bayar da sama da dala biliyan 21 kai tsaye ta hanyar taimakon soji, yayin da aka kai hare-hare kan Iran da Yemen da nufin karfafa matsayin Isra'ila.
A matakin siyasa, ana shirin kafa wani shiri wanda bisa ga shi ne za a ba da amanar gwamnatin Gaza ga wani "kwamiti a Falasdinu" da za su yi aiki karkashin kulawar wata kungiyar rikon kwarya ta kasa da kasa da ake kira "Komitin zaman lafiya". An ce wannan majalisar za ta kasance karkashin jagorancin Donald Trump kuma za ta hada da wasu mutane kamar Tony Blair; shirin da masu sukar suka yi dauke shi da cewa zai sake haifar da wani nau'i na sabon tsarin mulkin mallaka.
A sa'i daya kuma, an yi nuni da cewa, raunin da ake samu a fannin gwagwarmaya a yankin, musamman bayan sauyin siyasa a kasar Syria, da kuma samar da wani tsari na dogaro da kai a wannan kasa, ya shirya shimfidar wannan yanayi. Rahoton ya kammala da wani muhimmin magana, yana mai jaddada cewa, duk da yiwuwar dakatar da yakin, babu wata fa'ida a fili na yin hukunci da adalci ga wadanda suka aikata wannan laifi cikin kankanin lokaci.
***************
Ƙarshen Labarin
Your Comment