22 Oktoba 2025 - 21:45
Source: ABNA24
An Kawar Da Shugabannin ISIS A Iraki

Wani mamba a kwamitin tsaro da kariya na majalisar dokokin Iraki ya sanar da kawar da dimbin jigogi a cikin kungiyar ta ISIS da aka fi sani da jagororin kungiyar na tsatso na uku.

Kamfanin dillancin labarai na AhlulBaiti (ABNA): “Abbas Sarout” mamba ne na kwamitin tsaro da kariya na majalisar dokokin kasar Iraki ya jaddada cewa, jami’an tsaron kasar sun yi nasarar kawar da wadanda ake kira shugabannin kungiyar ISIS.

Ya kara da cewa: Ana daukar wadannan shugabanni a matsayin babban ginshikin kungiyar ta'addanci ta ISIS a shekarun baya-bayan nan. Kungiyar ISIS ta dogara da wadannan jagorori wajen gudanar da ayyukanta na aikata laifuka a wasu lardunan kasar Iraki, amma kokarin leken asirin da sojojin Irakin suka yi cikin shekaru uku da suka gabata ya sa aka kawar da mafi yawansu.

Sarout ya jaddada cewa: A halin yanzu, kungiyoyin ISIS na karkashin kasa ne kawai suka rage, suna fakewa a yankunan tsaunuka da hamada.

.................

Your Comment

You are replying to: .
captcha