23 Oktoba 2025 - 21:42
Source: ABNA24
Cikin Shekaru 2; Yadda Isra'ila Ta Jefa Tan Dubu 200 Na Bama-Bamai A Gaza

Tan dubu 200 na ababen fashewa — Isra’ila ta yi amfani da su a Gaza. A duk duniya, ana samar da tan 29,000 na TNT a shekara, amma Isra’ila cikin shekaru biyu ta yi amfani da abin da zai isa shekara bakwai na na Bama-Bamai da za a yi amfani da su a duniya.

Kamfanin dillancin labarain kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya kawo maku cewa: Daga 7 Oktoba 2023 zuwa 6 Oktoba 2025 = kwanaki 730 gaba ɗaya shekaru biyu cikakku na yaƙi da hallaka. Isra’ila ta jefa tan dubu 200 na bam-bam da harsasai a Gaza.

Wannan hoton da kuke gani ba Hiroshima bace a 1945… A’a! Wannan Gaza ce — ta hanyar harin da sojojin Isra’ila da makaman Amurka suka yi a cikin shekaru biyu da ake shafe ana yaƙi.

Bisa La’akari Da Cewa:

- Girman Gaza ya ninka ƙaramin yankin Hiroshima kusan sau uku, amma Isra’ila ta jefa mata makamashin da ya kai bom din nukiliya guda 8–10 irin na Hiroshima/Nagasaki!

- 548 ton na fashewa a kowanne kilomita murabba’i — wannan ita ce “ƙarfin lalacewar da ayyukan da Isra'ila take aitawarwa a Gaza.

Bisa ƙididdiga yawan jama’ar Gaza = mutane miliyan 2.23.

Wato kowane mutum — yaro, mace, dattijo — ya samu 90 kg na bam a kansa, nauyin mutum ɗaya!

Wannan ya ninka abin da aka yi wa Dresden, Jamus, fiye da sau 50, kuma a ƙarfi ya fi ta sau 40 bisa girman yankin.

Wannan ya nuna cewa abinda da yake faruwa a Gaza ya zarce duk wani abin da aka taɓa gani a tarihin yaƙe-yaƙe na zamani.

Tan dubu 200 na ababen fashewa — Isra’ila ta yi amfani da su a Gaza. A duk duniya, ana samar da tan 29,000 na TNT a shekara, amma Isra’ila cikin shekaru biyu ta yi amfani da abin da zai isa shekara bakwai na na Bama-Bamai da za a yi amfani da su a duniya.

Duk da waɗannan mayagun makamai masu nauyi da suka yi amfani da su a Gaza hakan bai sun cimma burinsu na kawar da Hamas ba.

- Tan dubu 200 na bam da aka jefa a Gaza, sun yi daidai da bom na nukiliya guda 13 irin na Hiroshima.

Waɗannan sun isa su rusa ƙasashe masu yawa gaba ɗaya!

Amma har yanzu Isra’ila ta kasa cimma burin Netanyahu na kawar da dakarun Hamas da ke kare ƙasar su da Isra'ila ta mamaya bisa haɗin kan Amurka da wasu daga cikin ƙasashe masu girman kai.

- A al’ada, ana auna fashewa da gram — domin gram kaɗan yana iya kashe mutum ɗaya ko raunata shi.

Amma Isra’ila ta jefa gram biliyan 200,000,000,000! Da aka raba wannan ga duk mutanen duniya, kowane mutum zai samu gram 24.3. Wannan yana nuna irin fasadi da zalunci da Isra’ila ta yi a duniya, da goyon bayan ƙasashe masu mugunta.

Tan dubu 200 na bam da aka jefa a Gaza sun ninka ƙarfin yaƙin Vietnam sau 20, duk da cewa Gaza tana da ƙananan girma sau 900. Sannan sun fi Dresden sau 25–27, da kuma Stalingrad sau 6.

Rahoton Hukuma Daga Gaza Bayan Shekaru Biyu:

Ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Hamas ya bayyana cewa Gaza na fuskantar kisan kare dangi da babbar annoba da keta haƙƙin ɗan Adam.

An lalata tare da rusa kashi 90% na Gaza gaba ɗaya ko rabin lalacewa.

Tan 200,000 na bam aka jefa.

Asibitoci 38 sun lalace ko sun daina aiki.

Makarantu 95% sun lalace.

Kashi 80% na yankin yana ƙarƙashin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Ƙiddigar Asarar Rayuka:

Mutane 76,639 sun yi shahada ko sun ɓace, ciki har da mutane 9,500 da ba a san inda suke ba.

Mutane 169,583 sun ji rauni, ciki har da 4800 an yanke gaɓobinsu, da 1200 sun zama guragu har abada.

12,000 mata cikin su ya zube saboda yunwa da rashin kula. 460 sun mutu saboda yunwa da rashin abinci.

Iyalai 2,700 sun ɓace gaba ɗaya daga rijistar jama’a.

Kusan Kowace Rana: Isra’ila tana kashe mutane 105, tana raunata 232, tana ɓacewa da mutane 13.

Jimilla:

76,639 su kai shahada

169,583 aka raunata

9,500 suka ɓace

Gaza ta rasa 6% na jama’arta cikin shekaru biyu (mutane miliyan 2.3).

Da Za Mu Fassara Haka:

– Kamar mutane miliyan 20 a Amurka,

ko miliyan 5 a Masar su mutu cikin shekaru biyu!

Wadannan ba lissafi bane kawai — rayuka ne da ake murƙushewa.

’Yan yara, mata, da dattawa suna mutuwa a ƙasa yayin da duniya ke kallon su.

Wannan Ba Yaƙi Bane – Kisan Kare Dangi Ne!

Tarihi ba zai taɓa yafewa ko yin shiru da ta’addanci ba.

Abin da ke faruwa a Gaza ba rikici bane, kisan ƙare dangi ne, bisa ƙa’idar dokokin duniya.

Lalacewar ta fi yadda aka auna. Ainihin adadin asarar rayuka ya fi wanda ake bayarwa.

“An la’anci waɗanda suka kafirce na daga cikin bani Isra’ila a harshen Dawuda da Isa ɗan Maryamu. Wannan tsinuwa saboda fasadin da suka. Sun kasance ba sa hanuwa daga mummunan abin da suke aikatawa….”.

(Surat al-Ma’ida 78–79)

Wannan Bala’i Ya Fi Ƙarfin Nukiliya.

Gaza tana ƙarƙashin ɗimbin bam.

Wannan abu bai taɓa faruwa ba a tarihin zamanin da muke ciki na ƙarni na 21 ba. Gaza tana ita ce babbar masifa ta ɗan Adam a wannan ƙarni.

Haj Emaad.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha