Kamfanin dillancin labarain kasa da kasa na AhlulBaiti (As) –ABNA-ya habarta cewa: Lebanon - musamman a tsakiyar yankunan arewacin ƙasar da yammacin Bekaa - ta na fuskantar ƙaruwar hare-hare da tashin hankali da damuwa a cikin 'yan kwanakin nan game da yiwuwar fafatawar soja da Isra’ila; saboda waɗannan yankuna suna fuskantar haɗarin hare-haren Sahyuniyawa.
Dangane da wannan, kafin azuhur a yau, jiragen yaƙin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a yankuna da dama a gabas da arewacin Lebanon, kuma sojojin mamaya sun yi iƙirarin cewa sun kai hari kan sansanin Hezbollah da cibiyar samar da makamai masu linzami a yankunan Bekaa da arewacin Lebanon.
Your Comment