1 Agusta 2020 - 11:13
Jagora : Kakaba Takunkumi Kan Wata Kasa, Aikata Manyan Laifuka Ne

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayyatollah Sayyid Ali Khamene’i, ya bayyana cewa kakaba takunkumi kan wata kasa tamakar aikata manyan laifuka ne.

ABNA: Ayyatollah Ali Khamene’I, na bayyana hakan ne a cikin jawabinsa da ya gabatar jiya Juma’a a zagayowar ranar babbar Sallah.

Ya kara da cewa makiyan Jamhuriyar Musulinci na Iran, na neman cimma manufofinsu, a cikin gajere, matsakaici da kuma dogon lokaci, ta hangar kakaba wa al’ummar Iran takunkumi.

Ya ce a cikin gajeren lokaci makiyan na son yin matsin lamba, domin al’umma ta damu har ta kai ga gajiya, duka wannan don hana kasa samun ci gaba a fanin kimiya.

Sannan makiyan na son su yanke alakar Iran da duk wasu ‘yan gwagwarmaya a yankin, saboda saninsu ne cewa Jamhuriyar Musulinci ta Iran za ta ci gaba da taimaka masu.

A wani share na jawabinsa, jagoran ya ce, daga karshe za’a yi galaba kan takunkuman, amma maganin hakan shi ne dogaro da kai da kuma karfin da kasa take da shi.

342/