5 Janairu 2020 - 05:03
Ana Juyayin Shahadar Janar Sulaimani Da Sauran Abokansa A Kasar Iraki

Kafafen yada labarai da dama a nan kasar Iran da wasu kasashen duniya suna watsa shirye-shiryen juyayi da kuma Jana’izan Shahidai Janar Sulaimani da Mahdi Muhandis a birnin Bagadaza da kuma Najaf da Karabala a kasar Iraqi.

(ABNA24.com) Kafafen yada labarai da dama a nan kasar Iran da wasu kasashen duniya suna watsa shirye-shiryen juyayi da kuma Jana’izan Shahidai Janar Sulaimani da Mahdi Muhandis a birnin Bagadaza da kuma Najaf da Karabala a kasar Iraqi.

Bayan girmama shahidan a cikin yankin “Green Zone “ na birnin Bagdaza a kasar ta Iraqi an kai gawawwakin shahidan zuwa haramin kazimai, daga nan kuma sai haramin Imam Husain a karbala sannan daga karshe haramin Imam Ali a Najaf a yau Asabar.

Ana sa ran za’a kawo da shahid Sulaimani da sauran shahidai Iraniyawa 5 zuwa gida a yammacin yau zuwa nan birnin Tehran kafin a fara shirye-shiryen na kasrshe don binnesu a garuruwansu na haihuwa.




/129