Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sakamakon hakan shi ne Shehbaz Sharif ya yanke shawarar rufe mashigai na ƙasa tsakanin Pakistan da Iran waɗanda manyan kayayyaki da kanana da samfuran makamashi ke wucewa ta cikinsu.
Nan take farashin kayayyaki ya ƙaru daga kashi 30 zuwa 50 cikin 100 sakamakon katsewar gas ɗin Iran, wanda Islamabad ke dogaro da shi da kashi 50 cikin 100 a kasuwar Pakistan, tare da wahalar samun madadi musamman tare da katsewa da raunin samarwa daga mashigar Hormuz.
Pakistan ta ba da hujjar matakin da ta dauke da cewa ta rufe mashigan ne don yaƙi da fataucin da ƙungiyoyin fataucin mutane da kwayoyi masu maye da sauransu daga dalilan tsaro ne ba na siyasa ba.
Iran ba ta amsa ko martani ba kuma ba ta yi sharhi kan komai ba, kawai tana lura da sawa lamarin ido da yanayin cikin gida na Pakistan da ya rasa samfuran makamashi na Iran, kuma farashin ya makamashi yana hauhawa da ƙaruwa cikin sauri.
Tattalin arzikin Pakistan tushensa yana cikin rikici, kuma aikin gudanar da tattalin arzikin gwamnatin Shehbaz ya cikin mayuwacin hali mai muni abin da ya haifar da bullar wasu zanga-zangogi.
Matsalar ita ce dangantakar Pakistan da Iran tana da tushe sosai, kuma akwai al'adu na haɗin gwiwa da manufofin haɗin gwiwa da tarihi na haɗayyar harshe wanda ake fahimta sosai, ban da hadayyar al’umma tsakanin ƙasashen biyu.
Biyayyar gwamnatin Pakistan ga Amurka tana sanya ta cikin rikici a gaban maƙwabtanta, wani rikici na tattalin arziki wanda Amurkawa ba za su magancewa Pakistan shi ba, kuma ba za su kashe kuɗi kan tattalin arzikin Pakistan ba, abin da ke nufin Amurka ta mamaye Pakistan kuma tana sarrafa gudanarwarta sosai, wannan shi ne abin da ake kira a nazarin siyasa da rufaffen mulkin mallaka.
A kiyasi abin da ke faruwa zai anfanar ga batun Imran Khan da masu adawar Pakistan da maƙiyan soji sosai, kuma duk lokacin da yanayin tattalin arzikin Pakistan ya tsananta, musamman bayan katsewar tushen makamashi na Iran, hakan zai ƙara tura al'ummar Pakistan cikin fushi da zargin gwamnatinsu da biyayya da mika wuya ga Trump ba tare da la'akari da muradun ƙasa ba.
A ra'ayinku shin wannan rikicin zai tsananta? Kuma shin Iran za ta ɗauki shawarar ta hukunta Pakistan a fannin tattalin arziki? Kuma shin tasirin hakan zai yaɗu kan ƙawancen Makka?.. Kuma a ƙarshe shin titunan Pakistan za su motsa don dakatar da wannan tsanantawa?
……………
Ra'ayinka