Mutane milyan 62 ne hukumar zaban kasar ta tattance da kuma za su bayyana zabin su tsawon kwanaki uku dangane da kawo gyara ga kudin tsarin mulkin kasar Masar, wata hanyar sake baiwa shugaban kasar mai ci Abdel Fattah-al Sissi cikakken mulki da kuma sake tsayawa takara a zaben shekarar 2024 zuwa shekara ta 2030.
Akasarin yan kasar sun yaba da wannan bukata daga Shugaban kasar ,lalurar su itace Shugaban kasar ya ci gaba da tabbatar da tsaro da kuma samarwa jama’a kayakin more rayuwa kamar dai yada aka saba gani a wannan tafiya da Shugaban kasar Abdel Fattah-al Sissi.
A shekara ta 2014 ne aka zabe Abdel Fattah-al Sissi da kusan kashi 96 cikin dari na kuri’u da aka kada,shekara daya bayan juyin mulki da sojojin kasar suka yiwa Mohamed Morsi.