A jawabinsa, ya bayyana taron IVC a matsayin lokaci mai muhimmanci na shirya yara. Ya ce, yayin da a makaranta ana koyar da yara ilimi su san harshe, su iya karatu, rubutu ko zane da sauran su, amma "Idan aka zo IVC, ana ƙoƙari ne a gyara tunaninsa ya zama yana tunani sahihi, ya san addini sahihi, ya fahimce shi sahihi." Ya kara da cewa, “ƙwaƙwalwa tana buƙatar a rayar da ita da tunani mai kyau".
Da yake jan hankalin yaran kan ilimi, ya bayyana ilimi a matsayin abu mai muhimmanci, tare da ƙarfafa su neman ilimi saboda Allah da kuma ilimi mai amfanarwa. Ya ce, “duk karatun da zai amfane ka duniya da lahira, ya kuma amfanar da al’umma, ibada ne.” Ilimin kiwon lafiya ne, noma, kimiyya, sufuri da sauran su, duk ibada ne, sai idan ba don Allah aka nema ba.
A ƙarshen jawabinsa, ya bayyana ilimi a matsayin ɗaya daga cikin dalilan nasarar Iran a yau da tsayuwarta ga kafircin duniya. Ya ƙarfafi yaran da su dage da neman ilimin da zai amfane su da al’umma, tare da samar da mafita ga matsalolin al'ummar.
Daga Ofishin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
23/08/2026
Ra'ayinka