Kasar Saudiyya ta ce tayi nasarar dakile barazanar da kungiyar Ansarullahi ta Houthi ke yi wa kasar Saudiyya daga Yemen.
Saboda haka kasar ta amince da zama da kungiyar Ansarullah tattaunawa a Teburin sulhu.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa Saudiyyar da 'yan korenta sun gano cewa Ansarullah za su gagare su ne, shi yasa ma suka amince da yin sulhun.
Saudiyya dai ta kasance kasa da tafi kowacce kusanci da Yemen.
A watan Janairun 2015 ne dai kungiyar Ansarullah wadanda suke samun goyon bayan al'ummar Yemen shiga babban birnin kasar wato San;a inda suka bukuci kafa kwamnati hadaka tare da hadin kan shugaban kasar wato Mansur Hadi wanda daga baya ya fice daga garin inda ya gudu zuwa Aden sannan ya nemi mafaka a kasar Saudiya.ABNA