Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Batun hikima a siyasar kasashen waje, shi ne ainihin mahadar hankalin siyasa da ka'idoji da dabi'u.
Batun hikima yana da matukar muhimmanci, kuma kuskurewa gareshi ba ya iya gyaruwa; misali, yanke kudiri na kuskure a siyasar cikin gida na iya dagula wa'adin shugabanci, amma yanke kudiri na kuskure a siyasar waje kamar rashin gane muhimanci da ma’anar zaman lafiya daga mika wuya, yana canza makomar tsatso da 'yancin kan al'ummai har abada.
Kullum dan siyasa maras hikima yana fuskantar tasirin tsoron yaki ko hayaniyar tattalin arziki; amma dan siyasa mai hikima, da hangen nesa mai nisa da nazarin ainihin niyyar makiya, yana tsallake siyasar yaudarar tunani ta makiya.
Zaman Lafiya; An Sharadanta Shi Ne Kasancewa Cikin Yardar Allah
A kan haka, za mu yi tsokaci kan daya daga cikin muhimman kalubale na siyasar kasashen waje da cikin gida wato "bambanci tsakanin zaman lafiya na dabaru da zaman lafiya na mika wuya" bisa ga nassosin addini.
Wasikar Imam Ali (AS) zuwa ga Malik Ashtar, ita ce mafi girma kuma mafi wadatarwar wasika a cikin Nahjul-Balagha game da mulki da siyasar gudanar da al'umma. A cikin wannan wasika an bayyana ginshikai da tushe, ka'idoji, hanyoyi, manufofi da kyawawan halaye na gudanarwa da mulki.
Daya daga cikin shahararrun nasihohin Imam Ali (AS) ga Malik Ashtar a cikin wannan wasika, shine bayyana iyaka tsakanin "zaman lafiya na hikima" da "zaman lafiya na wulakanci". Suna cewa: "Idan makiya suka gayyace ka zuwa wani zaman lafiya da ke da yardar Allah, ka karba saboda fa'idodi uku: hutawar sojoji da rage matsi kan dakaru, kawar da damuwar gwamnati da mayar da hankali kan harkokin cikin gida maimakon yaki, da kuma tsaron ƙasa don kare rayuka da dukiyoyin mutane."
Muhimmin abin lura a nan shi ne, ra'ayin Amiral-Mu'minin (AS) game da zaman lafiya, sharadi ne da yardar Allah, kuma baya hada da zaman lafiya da ke wulakanta Musulunci, rasa hakki, ko mika wuya ga karya.
Neman Yaki Da Mika Wuya, Haramun Ne!
Binciken tarihi ya nuna cewa Imam Ali (AS) bai taba neman yaki ba, amma a gaban fitina ko cin zarafin hakki, bai taba yin kasa a gwiwa ba. Suna cewa a Nahjil-Balagha: "Kada ku yake su sai sun fara yakarku; wato, kada ku fara yaki sai makiya sun fara" ; amma duk lokacin da aka tilasta musu yaki, sukan shiga fagen fama.
Mulki; Iyaka Tsakanin Zaman Lafiya Da Yaudara
Daya daga cikin muhimman misalan tarihin Musulunci da ke bayyana iyaka tsakanin zaman lafiya na gaskiya da zaman lafiya na yaudara, shi ne batun hukunci (yanke hukunci) a yakin Siffin, wanda sabanin yadda ake zato, ba rikici ne na gajeren lokaci ba, ya dauki tsawon watanni.
Karbar hukunci ko shiga tsakani daga bangaren Imam, ba zabi ne na dabaru don zaman lafiya ba; a'a, makirci ne daga makiya don kalubalantar ikon Imam da kuma samar da fagen wata babbar fitina.
Hukunci har ya kai ga an zargi shi a koyarwar Imamai Masu Tsarki (AS), har Imam Rida (AS) ya ce game da 'yan hukunci: "Wadanda suka taka rawa a hukunci, sun kasance a kan hanyar karkacewa."
Iran Da Manhajar Amiral-Mu'minin (AS)
A karshe za a iya yanke cewa idan aka gabatar da wani kudiri na zaman lafiya wanda ba ya kiyaye ka'idoji, 'yancin kan kasa da mutunta hakki, to shi dai kamar wannan hukunci na yaudara ne a yakin Siffin, kuma sam ba zaman lafiya ba ne; sai dai, wani nau'in mika wuya ne a karkashin tattaunawa.
Iran ba ta taba neman yaki ba kuma ba ta neman sa, amma a gaban zaman lafiya ko yaki da zai jawo asarar hakki da 'yancin kan kasa, za ta yi kamar yadda Amiral-Mu'minin (AS) ya yi.
…………
Ra'ayinka