9 Nuwamba 2026 - 20:03
Source: ABNA24
Haaretz: Cikakkiyar Rushewar Netanyahu a Gaban Kyamarori Rashin Tunaninsa Ya Bayyana

Jaridar Ibraniyawa Haaretz tare da yin nuni da bayanin da aka ɗauka na Benjamin Netanyahu, firaministan gwamnatin Sahayoniya, ta rubuta: abin da ya faru, cikakkiyar rushewa ce da wargajewa mabayyaniya a gaban kyamarori kuma yin anfani da kalmar "hysteria" wajen kwatanta yanayi ana ɗaukarta a matsayin Kalmar da aka takaita wajen siffan ta shi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Netanyahu da yammacin jiya tare da wallafa wata sanarwa da aka ɗauka ya bayyana; bayanin da sifanta shi da kalmar "hysteria" wajen kwatanta wanna lamari ma ana ɗaukarta a matsayin sassauƙa. Abin da ya faru, cikakkiyar rushewa da bayyananniyar wargajewarsa a gaban kyamarori.

Jaridar Ibraniyawa Haaretz ta rubuta: Benjamin Netanyahu yana ɗaga taken haɗin kai ne kawai lokacin da ya ji haɗarin rasa mulki yana yi masa barazana kuma faɗuwa daga matsayin firaminista ya fi kusanci gare shi fiye da kowane lokaci.

Haaretz a ci gaba ta rubuta: ko da lokacin da Netanyahu ya bayyana a matsayin mai kare haɗin kai, ba zai iya barin al'adarsa ta ƙarya da karkatar da tarihi, tarihin da ba shi da nisa sosai.

Wannan jaridar tare da yin nuni da wani kwatance mai ban mamaki da Netanyahu ya yi tsakanin yanayin Isra'ila da abubuwan da ke faruwa a Turai, ta rubuta cewa rashin daidaiton tunaninsa a cikin waɗannan maganganun ya bayyana.

Netanyahu ya ce: "Wuta da harshen wuta a titunan Paris da Brussels idan aka kwatanta da wutar da za mu gani a titunan Jerusalem, Tel Aviv da Haifa, za su bayyana a matsayin ba komai ba. Isra'ila ba za ta ƙara wanzuwa cikin sauƙi ba."

Haaretz a ƙarshe ta nanata cewa waɗannan maganganun sun yi daidai da yanayin tunanin firaministan Isra'ila.

..................

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha