30 Yuli 2026 - 14:57
Source: ABNA24
IRGC: Hafsoshi Da Ma’aikatan Jirage Sun Sheka Tare Da Lalata Jiragen Yaƙi Uku Na F-35 A Al-Azraq A Jordan

Sashen hulɗa da jama'a na Sojojin Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci a sanarwa mai lamba 55 ya sanar da cikakken lalata jiragen yaƙi uku na F-35 da kuma yi wa wasu uku mummunar barna da kashe wasu hafsoshi da ma'aikatan fasaha da gyara aAl-Azraq, a matsayin ramuwa ga harin ta’addancin Amurka ya yi a Qeshm.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Sashen hulɗa da jama'a na Sojojin Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci ya sanar: Da sanyin safiyar yau, abokiyar gaba Amurka, ta kai hari ta sama kan gidaje biyu na fararen hula a tsibirin Qeshm, tare da amfani da bama-bamai masu fashewa, ta kai hari kan gidaje biyu na mutanen yankin, wanda ya yi sanadin shahadar uba, uwa, da ɗa ɗaya daga cikin iyali, yayin da wasu yara biyu suka jikkata.

A matsayin ramuwa ga wannan laifi, da sanyin safiyar yau mayaƙan Sojojin sararin samaniya na Irgc sun kai hari kan wurin ajiyewa da rumfar gyaran jiragen F-35 na maƙiyin Amurka a sansanin sojin sama na Al-Azraq, tare da makamai masu linzami na ballistic da yawa, inda suka lalata jiragen F-35 uku gaba ɗaya, tare da yi wa wasu uku mummunar barna.

A wannan harin, wasu hafsoshi da ma'aikatan fasaha da gyara na maƙiyin su ma suka mutu.

Sun kara da cew: Yankin mu ba wurin sojojin da ke kashe yara ba ne, waɗanda suke azabtar da iyalai marasa laifi da wannan zalunci a tsakiyar dare suna barci. Yaƙinmu da ku zai ci gaba har sai mun kori mamayar Amurka ta ƙarshe daga ƙasashen Musulunci.

"Idan kuka taimaki Allah, zai taimake ku, kuma ya tabbatar da ƙafafunku."

»إِنْ تَنْصُرُوا اللَّهَ یَنْصُرْکُمْ وَ یُثَبِّتْ أَقْدَامَکُمْ«

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha