Martanin Iran
-
Iran Ta Lalata Na'urorin Radar Da Cibiyoyin Taron Makiya A Bahrain Da AUE
Ofishin Hulɗa da Jama'a na Sojojin Iran, ta hanyar fitar da wata sanarwa, ya ba da labarin aiwatar da mataki na 30 na "Harin Tsawa" wanda a cikinsa, jirage marasa matuki na "Arash" da dama sun kai hari ga na'urorin radar da wuraren da sojojin Amurka ke tsugunna a Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain.
-
IRGC: Ta Kai Hari Mai Tsanani Da Ƙarfi A Masaukin Kwamandojin Amurka A Sansanin Ali Al-Salim
Iran: Ta Kashe Wasu Kwamandojin Amurka Da Kune Jirage Marasa Matuka A Kuwait
Rundunar Tsaro ta Juyin Juya Hali a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa: Ta kone hedkwatar da wurin zaman kwamandojin Amurka na sansanin Ali Al-Salim, rumbun ajiyar jirage marasa matuki, da kuma wurin da ake ajiye jirage marasa matuki.
-
Iran Za Ta Mayar Da Martani Ga Hare-Haren Amurka Fiye Da Yadda Suka Yi
"Wata majiya ta soji mai girma ta jaddada cewa Iran za ta mayar da martani ga hare-haren 'yan ta'addan Amurka fiye da yadda suka yi."
-
Iran Ta Lalata Kayan Aikin Soji Da Wuraren Da Jiragen Yakin Makiya Suke Ajiye + Bidiyo
Rundunar Tsaro ta Juyin Juya Halin Musulunci ta sanar da cewa: An lalatar da kayan aikin fasaha da gyare-gyare da kuma wuraren da jiragen yakin makiya suke ajaiye a sansanonin sojan saman Amurka guda biyu na Malik Hussein da Al-Azraq.
-
IRGC: Sun Lalata Rumfunan Jirage Mara Matuki Guda Biyu Da Tankin Man Fetur A Sansanin Amurka A Kuwait
Dakarun Juyin Musulunci sun tabbatar da cewa, harin ya haifar da lalata rumfunan jirage mara matuki guda biyu, da tankin man fetur na jiragen sama da jirage masu saukar ungulu na soji a cikin sansanin.
-
Iran: Mun Shirya Babban Shiri Don Mayar Da Martani Ga Duk Wata Wautar Amurka Mai Yiwuwa
Mun Shirya Babban Tsari Don Mayar Da Martani Ga Duk Wata Wauta Ta Amurka Mai Yiwuwa
-
IRGC: Hafsoshi Da Ma’aikatan Jirage Sun Sheka Tare Da Lalata Jiragen Yaƙi Uku Na F-35 A Al-Azraq A Jordan
Sashen hulɗa da jama'a na Sojojin Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci a sanarwa mai lamba 55 ya sanar da cikakken lalata jiragen yaƙi uku na F-35 da kuma yi wa wasu uku mummunar barna da kashe wasu hafsoshi da ma'aikatan fasaha da gyara aAl-Azraq, a matsayin ramuwa ga harin ta’addancin Amurka ya yi a Qeshm.
-
Menene Amurka Ta Yi Hasara a Makon Da Ya Gabata?
Girman Asarar Amurka A Fafatawar Mako Guda Da Iran
Rahotannin da kafofin watsa labarai na kasashen yamma suka buga a 'yan kwanakin nan sun nuna cewa fafatawar baya-bayan nan da Iran, ta haifar da hasarar rayuka da soji mai yawa ga Amurka a yankin, kuma ta yi tasiri ga lissafin rashin dabarar yakin Washington.
-
Labarai Cikin Bidiyo | Na Hare-Haren Baya-Bayan Nan Na IRGC Ya Kawar Da Hadafofi Masu Muhimmanci
Dakarun Juyin Musulunci na Iran: Mun kai hari mai halakarwa a kan sansanin Amurka a Al-Azraq a Jordan, mun lalata na’urar tsaron sama nau'in Patriot da balloon na leken asiri a Arbil. Amurka mai kashe yara yana ƙarya a fili ga al'ummarsa da sauran mutane game da adadin wadanda suka mutu, kuma muna kira ga cibiyoyin bincike da kafofin yada labarai da su gudanar da bincike a fagen game da wannan.
-
Kanar Tajik: Hare-Haren Baya-Bayan Nan Na IRGC Ya Kawar Da Hadafofi Masu Muhimmanci
• Na'urar tsaro ta Patriot • Na’urar Balon leken asiri • Rumbun ajiye jiragen yaki • Wurin zaman sojoji • Hedikwatar 'yan ta'adda Duk sun kasance cikin jerin manufofin da aka lalata.
-
IRGC: Mun Lalata Na’urar Tsaron Sama Ta Patriot Da Na’urar Leken Asiri A Arbil
IRGC: Sojoji Da Dama Sun Sheka Da Raunatar Wasu A Mummmunan Hari Kan Sansanin Amurka A Al-Azraq A Jordan
Dakarun Juyin Musulunci na Iran: Mun kai hari mai halakarwa a kan sansanin Amurka a Al-Azraq a Jordan, mun lalata na’urar tsaron sama nau'in Patriot da balloon na leken asiri a Arbil. Amurka mai kashe yara yana ƙarya a fili ga al'ummarsa da sauran mutane game da adadin wadanda suka mutu, kuma muna kira ga cibiyoyin bincike da kafofin yada labarai da su gudanar da bincike a fagen game da wannan.
-
Khatam: Za Mu Kai Hari Kan Ababen More Rayuwar Man Fetur, Gas, Wutar Lantarki Da Tattalin Arzikin Yankin
Hedkwatar Khatamul-Anbiya ta yi gargadin cewa: Idan aka aiwatar da barazanar Amurka, sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za su yarda da fitar da ko digo ɗaya na man fetur ba, kuma za a kai hari a kan ababen more rayuwa na man fetur, gas, wutar lantarki da tattalin arziki na yankin.
-
Iran: Idan Har Aka Kai Hari Kan Gadoji Da Tashoshin Wutar Ƙasarmu Zamu Yanke Wutar Yankin
Kwamandan rundunar sararin samaniya na dakarun juyin musulunci na Iran, a cikin wani sako, ya bayyana cewa: Idan har aka kai hari a kan gadojinmu da tashoshin wutar lantarkinmu, to za mu yanke wutar lantarki ga kawaye da masu karbar bakuncin masu kashe yara.
-
Iran Na Ci Baba Da Kai Hare-Haren Jiragen Marasa Matuki Kan Sansanonin Amurka A Yankin
A zagaye na ashirin na aikin Tsawar Azaba, sa'o'i da suka gabata, jiragen mara matuki na sojoji, sun kai hari a kan sansanin Sheikh Isa na sojojin ta'adda na Amurka a Bahrain.
-
Iran: Yadda IRGC Suka Dibge Sansanoni Uku Na Amurka A Kuwait, Da Jirage Marasa Matuka
A zagaye na goma sha tara na aikin Tsawar Azaba, sansanonin Amurka na Ahmad Al-Jaber, Al-Udayri da sansanin Arifjan a Kuwait, sun fuskanci hare-haren jiragen mara matuki masu tarwatsa komai suka daka na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
IRGC: Baƙin Daren Ga Radars Da Na’urorin Tsaron Sama Na Amurka A Yankin
IRGC: Yadda Dakarun Iran Ska Lalata Radars Da Na’urorin Tsaron Sama Na Amurka Baƙin Daren Jiya A Yankin
Dakarun Juyin Musulunci na Iran, tare da fitar da wata sanarwa, sun sanar da cewa rundunar sararin samaniya ta dakarun juyin musulunci, sa'o'i cikin daren da ya gabata, ta maishe da wannan daren bakinkirir ga radars da na’urorin tsaron saman Amurka a yankin, a zagaye na 24 na aikin Nasr 2, da lambar sirrri mai albarka ta "Ya Ruqayya (A.S)," sun lalata wani radar Amurka a Al-Muharraq na Bahrain gaba daya, ta dena aiki, haka kuma sun kai hari na hadin gwiwa da makamai masu linzami da jirage mara matuki a kan wata na’urar tsaron sama ta Patriot na Amurka a Al-Rifa'a na Bahrain, tare da lalata ta.
-
Ba'amurken Marubuci: Trump Ya Mai Da Rayukan Sojojin Amurka Sadaukarwa A Yaƙin Sa Kai
Wani marubuci kuma manazarcin Amurka, yana mai sukar aikin Donald Trump a yaƙi da Iran, ya jaddada cewa shugaban Amurka har yanzu bai bayar da cikakken bayani game da manufofin wannan yaƙi da dalilin mutuwar sojojin Amurka ba, kuma ya jefa rayukan sojojin wannan ƙasa cikin hadarin "yaƙin d ya sa kansa."
-
Iran Ta Daidaita Makamanta Da Na’urorin Tsaron Amurka
Iran Tana Amfani Da Makamai Masu Linzami Masu Sauri Da Ƙarfin Motsi
Jaridar Wall Street Journal, ta nakalto daga jami'an Amurka, rahoton cewa Iran, ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu sauri da ƙarfin motsi, ta daidaita da tsarin na’urorin tsaron Amurka. An buga wannan rahoto ne a daidai lokacin da jami'an Amurka da sojojin wannan ƙasa da dama suka jikkata a hare-haren Iran na baya-bayan nan a kan sansanonin Amurka a Jordan, kuma sojoji biyu sun mutu. Hotunan tauraron dan adam sun tabbatar da lalata rumfunan shirya jiragen yaƙi a sansanin Muwaffaq al-Salti.
-
Cikakken Bayani Game Da Hare-Haren Iran A Kan Sansanin Sojojin Amurka A Jordan
Jaridar New York Times, ta nakalto daga jami'an Amurka, ta ba da rahoton cewa harin Iran na ranar Juma'a, shi ne hari na huɗu a cikin kwanaki biyar da suka gabata wanda ya kai hari kan sojojin Amurka a Jordan.
-
Iran: Sansanoni 2 Na Amurka A Kuwait Sun Sha Wuta A Hare-Haren Jirage Marasa Matuki
A mataki na goma sha shida na aikin Tsawar Azaba, sansanonin Ali Al-Salem da Al-Udayri na Kuwait, sun fuskanci hare-haren jirage marasa matuki masu lalata na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
-
Iran : Na Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Jirage Marasa Matuki Kan Sansanonin Amurka A Kuwait
A cikin sabon zagaye na hare-haren jirage marasa matuki na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a mataki na goma sha bakwai na aikin Tsawa, an sake kai hari a kan ɗakin ajiyar alburusai da rumfunan kayan aiki na sojojin ta'adda na Amurka a Kuwait a karo na biyu.
-
Iran Ta Yi Amfani Da Karamin Sashe Ne Kawai Na Ƙarfinta Akan Karfin Amurka
MTI: Bayan Vietnam Iran Ce Kawai Ta Kai Wa Amurka Irin Wannan Hare-hare Masu Barna
Alon Mizrahi, manazarcin tsaro na Isra'ila, a yau (Asabar) a cikin wani sako a shafin sada zumunta na X, ya yi nazari kan nagartar aikin sojin Iran wajen fuskantar sojojin Amurka. Kowane wuri na Amurka a yammacin Asiya an gano su, kowane sansani an kai masa hari, kuma dukkan cibiyoyinsu suna ƙarƙashin sa ido.
-
Reza'i: Yarjejeniyar Fahimtar Juna Ta ƙare | Za Mu Kai Hari Ko Ina Idan Ta'addancin Washington Ya Ci Gaba
Mai ba da shawarar soji ga jagoran juyin juya hali, Laftanar Janar Mohsen Reza'i, ya jaddada shirye-shiryen Iran don shiga matakin hari gaba daya idan ta'addancin ya ci gaba, yana mai nuni da cewa iƙirarin Washington na haɗin gwiwa wajen sarrafa mashigar Hurmuz ba abin karɓa ba ne a duniya.
-
IRGC: Sun Lalatar Na'urar Radar Mai Dogon Zango Da Tarin Jiragen Saman Dakon Man Fetur Na Amurka
Wannan aikin da nasararsa sadaukarwa ne ga shahidan da Amurka ta kaiwa hari baya-bayan nan, domin hukunta masu cin zarafi da kuma azabtar da sojojin Amurka masu kashe yara.
-
IRGC: Sun Lalata Radar Sarrafa Makamai Ta Ruwa Da Sama Na Amurka A Oman
Sannan Ofishin Hulda da Jama'a na Dakarun Juyin Musulunci na Iran a cikin sanarwa mai lamba 21 na aikin Nasr 2, da lambar sirri mai albarka ta "Ya Aba Abdillahil-Husain (A.S)," sun sanar da cewa:Sun kai hari tare da lalata radar sarrafa ruwa a kan duwatsun Salama, da radar sarrafa makamai ta sama ta Amurka da ke yankin Ghanam na Oman.
-
Iran: Ta Kai Hari Kan Cibiyar Umarni Ayyukan Amurka A Siriya
Dakarun Juyin Musulunci na Iran a cikin wata sanarwa sun ba da rahoton harin bazata da suka kai a kan cibiyar kwamandancin ayyuka na musamman na makiya a yankin Al-Tanf na Siriya, a matsayin ramuwa ga jinin sojojin shahidan Iran shahr.
-
Kafofin Larabawa: Iran Ta Kai Hari Mafi Muni A Bahrain
A cewar majiyoyi, an ji karar fashe-fashe da dama a Bahrain. An kuma sami fashe-fashe masu ƙarfi a sansanonin soji na Amurka a Jordan. Rahotanni sun nuna cewa, bayan waɗannan abubuwan, an ƙarfafa tsaro a yankin kuma an ƙara ayyukan soji na Amurka.
-
Iran; Ta Aike Da Sako Ga Al'ummar Jordan
Iran: Ta Kai Hari A Kan Cibiyar Umarni Da Sarrafawa Ta Amurka A Jordan
Rundunar sararin samaniya ta dakarun juyin musulunci ta kai hari a kan sansanin Al-Azraq na Jordan da makamai masu linzami na "Khaibar Shikan," kuma ta yi kira ga al'ummar Jordan da su kai hari ga muradun Amurka yar mamaya su tsarkake ƙasarsu daga gare su.
-
Bidiyo | Yadda Makamai Masu Linzami 4 Suka Sauka Kan Sansanin Sojan Saman Malik Faisal A Jordan
Abin ban sha'awa a cikin wannan lamari shi ne, ba wai kawai makamai masu linzami na tsaro masu tsada sun kasa fuskantar makaman Iran ba, a'a, sai dai ma da alama daya daga cikin makaman ya lalata nau’rar tsaro da kansa, domin bayan harba shi, ba a sake harba wani makami na tsaro daga na’urar ba.
-
IRGC: Sun Babbake Cibiyar KJL Babban Tushe Na Kai Daukin Sojojin Amurka A Kuwait
Dakarun Juyin Musulunci: sun babbake KJL, babbar cibiyar shirya da tallafi na sojojin Amurka a Yammacin Asiya a Mina Abdullah na Kuwait.