29 Yuli 2026 - 14:46
Source: ABNA24
Dakarun Hashdush-Sha'abi Sama Da 52 Ne Harin Amurka Da Saudiyya Ya Rutsa Da Su Iraqi

Shahadar mayaƙa aƙalla 20, kuma wasu 32 sun sami raunuka, sakamakon farko ba na ƙarshe ba na hare-haren ta'addancin haɗin gwiwar Amurka da Saudiyya wanda suka kai a sassa daban-daban biranen Iraqi, wanda ya shafi wasu cibiyoyi na hukuma na Hashdush-Sha'abi) a wasu larduna na Iraki.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa:  Kamar yadda bayanan da aka tattara suka nuna, hare-haren sun shafi cibiyoyin dakarun a lardunan Bagadaza, Wasit, Ninawa, Basra, Kirkuk, Karbala, da Diyala, wanda kuma ya haifar da barnar kayan aiki dabam-dabam ga wasu cibiyoyi da motoci da kayan aikin soja.
Dakarun Hashdush-Sha'abi sun jaddada cewa kwamitocin da suka dace suna ci gaba da ayyukansu na fage don ƙididdige barnar da kuma tantance bayanai, saboda haka, adadin shahidan da waɗanda suka jikkata da aka sanar sakamako ne na farko wanda zai iya ƙaruwa ko sabuntawa yayin da ake ci gaba da ayyukan bincike da tantancewa da kuma kammala rahotannin fagagen da Hare-haren suka shafa.
Hashdush-Sha'abi)
29 ga Yuli, 2026

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha