ABNA24 : Wannan bayanin na kunshe ne a sanarwar bayan taron da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka fitar, yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Siriya ya kawo a Tehran.
Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawwad Zarif, ya ce yana da kyau a rika samun irin wannan tattaunawa lokaci zuwa lokaci tsakani Iran da Siriya dama wasu kasashe.
A nashi bangare ministan harkokin wajen kasar ta Siriya, Faisal Mekdad, godewa Iran ya yi game da irin goyan bayan da take baiwa kasarsa kan yaki da ta’addanci da tsatsauran ra’ayi.
A daya bangaren ya kuma isar da sakon ta’aziyya na shugaban Bashar Al-Assad da al’ummar Siriya, game da kisan masanin nukiliyar kasar ta Iran Mohsen Fakhrizadeh.
342/