19 Disamba 2015 - 12:23
Harin Zariya;  Sarkin Saudiyyah a wane taragon yake?

Ganin yadda dimbin malaman addinin musulunci da suka fito daga bangarori daban daban na Nigeria da kuma kuma mazhabobi dban daban na Ahlul Sunnah na cikin gida da sauran kasashe na duniya suka fito suka bayyana matsayin su akan harin ta'addancin sojoi a Zariya inda suka bayyana tir da Allah waddai.

Kan wannan abu, yasa al'umma suna tambaya suna ganin cewa shi sarkin Saudiyyah Salman bin Abdulaziz Al Saud a wane tarago yake?

Jama'atu Nasril Islam kungiya data kunshi malamai daga mazhaobi daban daban da dariku daban daban a Nigeria, da kuma majalisar koli ta kula da al'amarin musulmi suma majalisa data kunshi malamai daban daban na kasa da suka fito daga mazhabobi daban daban duk sun yi tir da wannan hare-haren da kira akan ayi bincike.

Amma Sarkin Saudiyyah Salman bin Abdulaziz Al Saud ya fito fili ne yana goyon bayan ta'addancin Sojoji akan Harkar Musulunci kuma ya siffanta wannan da fada da ta'addanci.

Salman bin Abdulaziz Al Saud ya bayyana haka ne a lokacin da yake Magana da shugaban kasar Nigeria ta wayar tarho a karo na farko tun bayan soma wannan  hare-haren na ta'addanci.

Kada a manta a lokacin wannan ta'addancin na sojoji babu irin hurumi na musulunci da basu taka ba, ciki kuwa harda cire Hijabin 'yan uwa mata da karfi a lokacin da suka kai su barikin su a Zariya, sannan suka muzanta su suna wulakanta Hijabin.288