8 Mayu 2025 - 20:34
Source: ABNA24
Qassam Sun Kai Munanan Hare-haren Kan Sojojin Isra'ila

Mummunan fashewar a Rafah ta faru ne akan Sojojin yahudawan sahyoniya wanda biyu daga ciki duka mutu nan take biyar suka jikkata 7

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: Dakarun Qassam sun sanar a cikin wata sanarwa cewa, a ci gaba da aikin Operation na "Kofofin Jahannama" sun tayar da wani katon bam a kusa da masallacin Umar bin Abdulaziz da ke unguwar Al-Tanour a Rafah. Fashewar ta kashe tare da jikkata sojojin yahudawan sahyoniya 7, kuma hotunan da ke cikin hoton da aka nuna sun nuna gutsutsutsurarrun jikinsu a warwatse.

Bayan faruwa lamarin anga yadda aka dauke sojojin sahayoniya da suka samu raunuka zuwa asibitin Kudus bayan da aka yi musu kwantan bauna a Rafah.

Kafofin yada labaran yahudanci sun bayar da rahoton kai wasu sojojin yahudawan sahyoniya nan take zuwa asibitin "Tashari Tsidiq" da ke birnin Kudus.

Wadannan masu raunukan sun samu munanan raunuka bayan wasu munanan hare-haren kwantan bauna da gwagwarmayar Palastinawa suka yi a kudancin Rafah.

Cikakkun bayanai na farmakin yau da mayakan 'yan Gwagwarmaya suka kai wa sojojin yahudawan sahyuniya a kudancin zirin Gaza

Rundunar Izzad-Din Qassam reshen soja na kungiyar Hamas ta sanar da cewa: Mayakan Qassam sun yi nasarar kai farmaki kan wasu gungun sojoji 12 na sashin injiniyancin sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da suke shirin tarwatsa wani gida da ke kusa da mahadar Al-Fida'i a unguwar Al-Tanour da ke gabashin birnin Rafah a kudancin zirin Gaza, tare da wasu makamai masu linzami guda biyu.

Majiyoyin yaren yahudanci sun rawaito cewa adadin wadanda suka mutu a cikin birged Golani na sojojin haramtacciyar Isra'ila sakamakon fashewar da ta auku tare da rugujewar ginin da wasu gungun sojoji suke a wurin ya karu zuwa 2 sannan wasu 5 sun jikkata, 4 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Your Comment

You are replying to: .
captcha