Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An danganta jirgin ruwan da Venezuela kuma an kama shi kusa da gabar tekun arewa maso gabashin Amurka ta Kudu, wanda shine karo na hudu da aka kwace irin wannan jirgin a cikin 'yan makonnin nan.
Rasha ta maida martani kan kwace jirgin Marinera da Amurka ta yi tana mai cewa: An ba wa Marinera lasisin wucin gadi mai tutar Rasha a ranar 24 ga Disamba.
Sojojin Amurka sun shiga jirgin Marinera a cikin ruwan kasa da kasa, wanda hakan ya saba wa tanadin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan Dokar Teku ta 1982.
Ita kuwa Birtaniya tana goyon bayan fashin jiragen ruwan da Amurka ta yi inda Ma'aikatar Tsaro ta Burtaniya ta tabbatar da goyon bayanta ga Amurka a aikin kwace jirgin ruwan mai "Bella 1".
Mujallar Foreign Policy ta buga wani bincike da ke cewa: Duk da ikirarin Trump na mamaye Venezuela amma abin mamaki, rahotanni daga ƙasar sun nuna cewa jami'an tsaro masu biyayya ga Maduro har yanzu suna nan a titunan babban birnin ƙasar da sauran biranen ƙasar, kuma babu rahotanni ko alamun zanga-zangar adawa.
Da alama Trump ya mayar da cirewa tare da sace Maduro a matsayin wani aiki na kashin kansa, ba tare da wani shiri na kawo sauyi ba.
Your Comment