Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya kawo maku cewa: Cibiyar Bayanai ta Hedikwatar Jami'in 'Yan Sanda na Tehran ta sanar da cewa: Tare da bin matakan leƙen asiri na musamman da kuma cikakken sa ido kan ayyuka, jami'an Ƙungiyar Leken Asiri ta 'Yan Sandan Babban Birnin sun yi nasarar gano maɓoyar wasu da ake zargi da hannu a tarzomar da aka yi kwanan nan a Tehran.
A yayin binciken waɗannan maɓoyar, an gano muggan makamai da makamai ƙanana, harsasai, da kayan da ake amfani da su wajen yin bama-bamai a gida kuma an kwace su.
Wannan nasarar ayyukan suna ci gaba da gudanar a dukkan sassan ƙasar Iran domin kare al'umma daga hare-haren ƴan ta'addan da suke don tada zaune tsaye.
Your Comment