Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sojojin Isra'ila sun sanar da cewa sun kai hari kan wasu wurare da suka yi ikirarin mallakar Hamas da Hizbullah ne a yankuna daban-daban na Lebanon.
Majiyoyin labarai sun ruwaito a yau Litinin cewa gwamnatin Isra'ila ta kai hari kan kauyen Ain Al-Tina a yankin Bekaa a gabashin Lebanon.
Kafofin watsa labaran Isra'ila sun kuma sanar da cewa sojojin sun kai hari kan kudancin Lebanon.
Kamar yadda Wakilin Al-Jazeera ya bayyana cewa gwamnatin Isra'ila ta kuma kai hari kan kauyen Anan a birnin Jizin a kudancin Lebanon.
Ya ce Isra'ila ta kai hari kan kauyukan Ain Al-Tina da Al-Manara a yankin Bekaa a gabashin Lebanon da kuma Anan a kudancin Lebanon a manyan hare-hare uku.
Sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa sun kai hari kan wasu wurare na Hamas da Hizbullah a Lebanon.
Isra'ila ta kai hari kan kauyen Kafrahti a kudancin Lebanon.
Bayanan nan, rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa tana da niyyar kai hari kan wasu wurare da ta yi ikirarin mallakar Hizbullah ne.
Your Comment