2 Disamba 2021 - 12:57
Imam Khamene'i: Masu Da'awar Kare Hakkin Dan Adam Suna Goyon Ta'asar Da Saddam Ya Aikata

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa a lokacinda Sadam Husain na kasar Iraki yake aikata ta’asar da ya aikata kan mutanen kasar Iran kungiyoyi da kasashe masu riya kare hakkin bil’adama suna goyon bayan abinda ya aikata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shafin yanar gizo na labarai, na ofishin jagoran ya bayyana haka a labarin da aka sanya a safiyar yau Alhamis na wata ganawar da jagoran yayi da kwamitin shahidan 3000 na garin Ilam a ranar 30 ga watan Aban da ya gabata.

Jagoran ya kara da cewa a lokacin da sojojin Sadam Hussain suka yi barin boma-bomai kan filin wasan kwallon kafa na garin Ilam a ranar 23 ga watan Bahman na shekara ta 1365 hijira shamsiyya, yayi haka ne tare da goyon bayan wadannan kasashe da kuma kungiyoyin masu riya kare hakkin bil’adama a duniya.

Daga karshe jagoran ya bukaci masu rubutu da magana su yi rubutu ko su yi magana su fadawa duniya irin ta’asan da Sadan Husain ya aikata a lokacinda sojojinsa suka yi ruwan boma-bomai kan filin wasanni na garin Ilam, inda ya kashe dubban ‘yan wasa da masu kallo.

Don haka dole ne duniya ta san wannan ta’asar wacce kasashen masu riya kare hakkin bil’adama suka yi shiru a kanta.

Banda kisan mutanme a filin wasa sojojin Sadam sun shiga gida-gida inda suka kashe mutane da dama, daga cikin har da shahid Rizayi Najad a gaban matarsa da kuma karamin diyarsa.

342/