29 Oktoba 2026 - 14:15
Source: Al-Mayadeen
Isra’ila Na Ci Gaba Da Mamayewarta A Al-Khalil A Rana Ta 7 Tare Da Raunata Da Kama Falasɗinawa

Isra’ila ta raunata Falasɗinawa biyu kuma da kama wasu 7 a ci gaba da mamayewar a jere a kwana 7 a Al-Khalil a Yammacin Kogin Jordan, a tsakiyar tilastawa yin ƙaura da killace mutane 5,000 duk da ƙoƙarin da kwamitocin agaji ke ci gaba da yi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sojojin Isra’ila sun jiwa Falasɗinawa biyu rauni, kuma sun kama Falasɗinawa bakwai, a yau Alhamis, a cikin mamayewarsu da ke ci gaba na kwana na bakwai a jere kan lardin Al-Khalil a Yammacin Kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu "Wafa" ya bayyana cewa sojojin mamayar sun kai wa Falasɗinawa Ahmad Abu Hishhash hari kai tsaye bayan sun shiga gidansa a garin Dura a kudancin Al-Khalil da bincike da lalata abubuwan da ke cikinsa, abin da ya haifar da raunata fuskarsa.

A yankin Wadi Al-Samn, Bafalasɗine Zain al-Din Abu Arram an ji masa rauni ƙwanƙwasa da kuna sakamakon dukan da sojojin mamayar suka yi masa, kuma an kai shi asibitin gwamnati na Yatta don samun jinya.

Majiyoyin tsaro sun gaya wa "Wafa" cewa sojojin mamayar sun kama Falasɗinawa 5, daga birnin Al-Khalil bayan binciken gidajensu da lalata abubuwan da ke cikinsu. Sun kuma kama 'yan'uwa biyu a lokacin da suke noma filayensu a yankin Arjum Ali a gabashin Yatta a kudancin lardin.

Sojojin mamayar Isra'ila sun kai farmaki kan gidajen Falasɗinawa da dama a garuruwan Taffuh da Halhul, sun yi masu mummunan barna kuma sun lalata abubuwan da ke cikinsu.

A wani yanayi mai alaƙa, Yahudawa sun kai hari kan Falasɗinawa da motocinsu a yankin Ras Al-Joura a ƙofar arewacin birnin Al-Khalil, wadda aka rufe tun farkon mamayewar ranar Juma'a da ta gabata.

Killacewa Da Tilasta Yin Ƙaura Da Rikicin Ɗan Adam

Sojojin mamayar na ci gaba da sanya tsananin killacewa kan lardin da rufe mashigunsa, musamman yankunan Al-Jalda da Deir Baha waɗanda ke ƙarƙashin cikakken rufewa da farmaki na yau da kullum. Mamayar ta tilasta wa wasu iyalai ƙaura daga gidajensu, yayin da take kewaye da wasu iyalai a ciki kuma tana hana su fita.

Dangane da bayanan kwamitin bibiya da tallafawa da karamar hukumar Al-Khalil, adadin iyalan da abin ya shafa ya kai kusan iyalai 780, yayin da adadin waɗanda aka tilasta musu ƙaura da aka kewaye ya kai kusan Falasɗinawa 5,000.

Duk da ƙuntatawar mamayar da hana isar da agaji a yammacin birnin, kwamitin tallafawa da agaji na ci gaba da ƙoƙarinsa wajin samar da kayan gaggawa. Shugaban kwamitin Sufyan Al-Muhtasib ya tabbatar wa "Wafa" cewa kwamitin ya yi nasarar samar da buƙatun kusan iyalai 700 na mafaka na wucin gadi da kayan abinci da magunguna, yana mai nuni da matsananciyar buƙatar samar da mafaka na wucin gadi ga ƙarin iyalai 135, ban da magungunan cututtuka masu tsayi da fakiti 700 na abinci kowace rana.

Al-Muhtasib ya yi gargaɗi kan yiyuwar ninka wahalar tare da ci gaba da samun kira na neman taimako daga waɗanda aka kewaye  su a yanayin hana motsawa da kawo cikas ga ƙungiyoyin agaji.

…………

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha