Har ila yau Nikzad ya yi kira da a kare hakkokin Falasdinawa da ake zalunta. Ya kuma kara da cewa haramtacciyar kasar Amurka ta tafka muggan laifukan yaki, saboda goyon bayan da take bawa yahuwan kan Falasdinawa.
Ya ce bisa amfani da siyasar nuna son kai da Amurka take yi, ya sa kawayenta, musamman HKI a matsayinta na babbar cibiyar ta’adanci ta duniya tana tafka laifukan yaki da suka hada sa kera makaman kare dangi da samar da kungiyoyin yan ta’adda da take hakkin dan adam a fili, tare da gallazawa kasashe masu neman yanci ta hanyar fakewa da Zargin karya.
An kafa kungiyar yan majalisun dokoki ne a shekara ta 1889, kuma dukkan majalisun kasashe 178 ne mambobi a majalisar hada kan kasashen duniya, yayinda wasu majalisun dokoki guda 12 na yanki aka zabesu a matsayin masu sa ido.
342/