15 Satumba 2021 - 11:26
​Isra’ila Ta Mikawa Falasdinawa A Gaza Alluran Riga Kafin Covid 19, 50,000 Lalatattu

Ma’aikatar kiwon lafiya a yankin zirin Gaza na kasar falasdinu da aka mamaye ta bada sanarwan cewa haramtacciyar kasar Isar’ila ta mika mata alluran riga kafin cutar covet 19 wadanda suka lalace.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shafin yanar gizo na larabarai Arab48 ya bayyana cewa a jiya litinin ce ma’aikatar lafiyar ta kammala aikin binciken alluran riga kafin 50,000 wadanda aka shigo da su ta kofar shiga yankin na Gaza mai suna ‘Karem Abu Salem, inda suka tabbatat cewa duk sun lalace saboda rashin kula da wurin ajiyesu da kuma jinkiri wajen mika su.

Kafin haka dai yahudawan sun bada sanarwan cewa za su mika alluran riga kafin samfurin Sputnik light ta kasar Rasha ga hukumomi a Gaza, amma sun ki bada su cikin lokaci sannan basu kula da wajen ajiyesu ba har suka lalace.

Tun bayan bullar cutar covid 19 a yankin Gaza dai mutane 147,368 ne suka kamu da cutar, kuma mutane 1,228 daga cikinsu sun rasa rayukansu. Sannan ya zuwa yanzu an yiwa mutane 354,000 ne kawai alluran riga kafin cutar. Yankin Gaza na da mutane kimani mil;iyon biyu.

342/