28 Agusta 2021 - 11:18
​Abdollahian: Iran Tana Maraba Da Yunkurin Iraki Domin Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdollahian ya bayyana cewa, kasarsa tana maraba da duk wani yunkuri daga bangaren kasar Iraki, domin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana hakan ne a daren jiya kafin ya kama hanya zuwa birnin Bagadaza na kasar Iraki, inda ya jaddada cewa, kasar Iraki tana da gagarumar rawar da za ta taka a bangarori daban-daban da suka shafi yankin gabas ta tsakiya, kuma kasar Iran har kullum a shirye take ta yi kafada da kafada tare da Iraki domin ganin an cimma wannan manufa.

Dangane da zaman taron kasashe makwabtan kasar Iraki da za a gudanar a birnin Bagadaza kuwa, Abdollahian ya bayyana cewa taron yana da matukar muhimmanci, kuma zai yi tasiri matuka wajen kara karfafa alakoki da ke tsakanin kasashe da ke makwabtaka da Iraki da ma sauran kasashen yankin gabas ta tsakiya.

342/